Daga Adamu Isah Jauro. A lokacin da naji Duniyar Social Media ta dau dumin bada labarin mutuwar wannan yaro, nan take na fara bincike kan ra...
Daga Adamu Isah Jauro.
A lokacin da naji Duniyar Social Media ta dau
dumin bada labarin mutuwar wannan yaro, nan
take na fara bincike kan rayuwar sa. Abinda bincikena ya tabbatar min shine: Wannan
yaro mawaki ne wanda ake mishi take da 'Dan
Autan Mawaka.
Nayi takaici matuka da naga wannan bayani, ace
yaron da alama ke nuna bai balaga ba, dan
musulmai a Arewacin Nigeria ya zama mawaki irin mawakan turawa har ya shahara a duniya,
wallahi wannan abun bakin ciki ne ga
al'ummarmu. Domin inada tabbas da yayi tsawon
rayuwa, to da yayi rayuwa mara anfani ga
al'umma.
Amma da yake Allah Ra'ufur Rahim ne sai ya dauki rayuwarsa tun gabanin ya balaga, gabanin
shari'a ta hau kan sa.
Ina rokon Allah ya gafarta masa yasa Aljannah
makomarsa da mu baki daya. Allah ka tsare
mana zuriyarmu daga tanbadewa Ameen.
COMMENTS