Watarana wani yaro yazo ya taradda mahaifiyarsa tana zubda qwalla sai yake tambayarta cewa: "Umma menene yasa kike saurin zubda hawayen...
Watarana wani yaro yazo ya
taradda mahaifiyarsa tana zubda
qwalla sai yake tambayarta cewa: "Umma menene yasa kike saurin
zubda hawayenki?". Sai mahaifiyarsa tasa tace dashi: "saboda inason yin kukanne
kawai". Yaron sai yace: "Ummah ban
gane meye kike nufi ba". Sai mahaifiyarsa tasa ta
rungumeshi tace dashi: "ae
bazaka ganeba
Daga bisani sai yaron yaje ya
taradda mahaifinshi yace dashi: "Abba ko menene yasa Ummah
take saurin kuka haka?". Sai mahaifinshi yace dashi: "Rabu
dasu ita haka kawai saita damu
mitane da kuka babu gaira babu
dalili ". Yaron sai yaji amsar tamar wani
iri. Dayaje makarantar islamiyya
sai ya ke tambayar malaminsu
cewa: "Mallam ko menene yasa
mata ke saurin kuka da wuri
haka?". Sai malaminsu yace dashi:
"lokacin da Allahu Azza wa Jalla
Ya halicci mace, sai ya sanyata ta
zamto wata halitta ta
musamman, Ya bata Karfin halin
daure duk wata wahala data shafi daukar ciki da goyon ciki
har haihuwa, Ya kuma bata
juriyar cigaba da fafutuka wajen
tarbiyar 'ya'yanta lokacin da
kowa ya gaza. Ya kuma bata
Hankalin taso da iyalenta acikin kowani yanayi, Ya bata hankali
tagane cewa miji nagari bazai
cutar da matarsa ba, sai dai wani
lokacin Ya kan jarabceta yaga
juriyarta. Sannan sai kuma Allah Ya bata
hawaye. Wannan hawayen
natane, baiwar tane, da zata iya
amfani dashi a lokacin dataso, a
inda taso, bata buqatar ta
bayanna menene yasa take kukan". Sai malamin yaci gaba da cewa:
"yakai wannan yaron, kyawun
mace ba'a tufafinta yake ba, ba
kuma a fuskarta yake ba, ko
kuma yadda take gyara gashinta,
a'a kyawunta yananan zaka ganshi a idanuwanta domin
sune madubin ganin xuciyarta,
ita kuma xuciya itace taskar dake
ajiye xunxurutun so. Don haka
daga zarar mace taga za'a samu
matsala a harkokin zamantakewa, sai tasoma kuka
ko tafara xubarda qwalla, domin
tasan duk wanda rai zaiyiwa
dadi ba ran mai shine". Allah Sarki mata iyayenmu
sarakunan tausayi. Allah Ya saka muku da alheri a
bisa dawainiyyar da kukeyi
damu.
COMMENTS