Assalamu alaikum kamar yadda ka sani ana iya samun wannan matsalar wato zakaga memory yana dauke da security da zarar ka sanyashi a waya sai...
Assalamu alaikum kamar yadda ka sani ana iya samun wannan matsalar wato zakaga memory yana dauke da security da zarar ka sanyashi a waya sai ace saika sanya wannan security kai kuma baka saniba kokuma ka manta to idan irin wannan abin ya faru, wasu suna yin amfani da wayar symbian domin suyi format dinsa idan anyi format din sai security ya fita amma duk de ba yadda aka soba domin kayi missing din abubuwanka da suke kan memory,
To Alhamdulillah yanzu sauki yaxo ita wannan hanya dazan bayar babu ruwanka dayin format na memory balle harka Rasa kayanka ita hanyar kawai zaka gano password dinka sannan kazo ka sanyashi saiya bude kokuma ka rufeshi kwata kwata,
Abin da zakayi kawai shine ka dora memory wanda yake dauke da password din akan wayarka ta android bayan ka dora yanzu kawai sai kayi download na ES EXPLORE.apk zaka iya download dinta a google kokuma play store, bayan ka dauko wannan application na es explore to saika budeshi idan ya bude saika shiga E wato memory saika duba zakaga gida gida kokuma ince folders to saika duba folder mai suna SYSTEM saika shigeta idan ta bude saika duba folder mai suna mmcstore to abin da zakayi anan kawai sai kayi Rename na mmcstore ka karawa folder .txt agabanta wato zata koma mmcstore.txt bayan ka gama Rename dinta shikkenan saika budeta ka duba ciki zakaga password din memory ka shikkenan sai kayi copy dinsa kaje file manager dinka ka shiga option ka cire kokuma kayi Remove password shikkenan ka gama
Allah ya bada sa,a
COMMENTS