Assalamu alaikum yan,uwa ma,abota harkar social network kada ku gaji da surutuna kwanakin baya nayi bayani akan yan 419 da yadda suke shirya...
Assalamu alaikum yan,uwa ma,abota harkar social network kada ku gaji da surutuna kwanakin baya nayi bayani akan yan 419 da yadda suke shirya danfara suke xaluntar mutane su mallake wani abu daga hannun mutane kamar kudi da sauran wasu abubuwan, to Alhamdulillah mutane da dama sun fahinci irin wannan mutanen kuma sun kiyaye sannan sun sake sanar da wadanda basu saniba, yanxu Alhamdulillah kusan kowa ya gane irin wannan yaudaran da sukeyi wanda suke mata take da ARASHIN TAYI AKAN BAR ARAHA wanda xakuji sunce yanxu haka suna da 25,00000 a wayansu ko fiye da haka suna cewa a aika da sakon message a rubuta lambobin katin sai a aikasu xuwa wasu lambobinsu wanda wannan lambobin da sukace ku aika sakon idan kun duba xakuga lambar wayansune da xarar kun aika wannan sakon kai tsaye xai tafi ixuwa wayansu, sukuma kafin ku farga xasuyi sauri su sa, nasan dayawa mutane yanxu sun gane wannan,
To ganin yadda yan 419 suka fahinci yanxu an fara ganosu shine suka sake bude wata sabuwar hanyar da xasuna yaudaran mutane suna karban kudinsu wato wannan hanyar ta dade wasunku sun riga da sun santa wasu kuma yanxu haka agunsu bakuwace to komade minene yanxu sinikom zai sanar daku yadda abin yake,
Hanyar da sukebi ba wani boyayyiyar hanya bane hanyar itace yanxu suna gina website ne wanda xasumar design kamar website din na campany layinne xakuga sun gina shafi wato website kalar na layukan kamar su MTN ETISALAT AIRTEL GLO xakuga site din yadau color kamar na ainihin sim dinne to abin ba haka yakeba kawai salone ya yaudara sabo da haka idan kukaci garo da irin wadannan shafukan to ku kula dakyau, yadda xaku gane na masu 419 ne da farko xakuga suna tallansa suna cewa for free browsing ko domin samun bunus shiga nan saisusa sunan site din,
Abin lura anan baxaku taba ganin campanin layi da kansaba yana tallan wai a shiga shafinsaba,
Sannan suna cewa xakusamu bunus
a layukan nigeria babu layin da suke tallan wai xaka samu kudi mai yawaba idan ka shiga shafin
Sannan idan kun shiga shafin xakuga gunsa number waya saiku aika sannan kuga gun sake sa number da kuma pin wato Rechage card to idan kuka lura babu wani shafi na Na layuka da suke umartar da asa kati xasuba da bunus sabo da haka wannan kadai ya isa ya tabbatar muku da irin wadannan yan 419 din sabo da haka dan Allah yan,uwa mukula sosai sannan mu kiyaye irin wadannan abubuwan domin kaucewa asara da fadawa sharrin yan 419, sannan ga wani shafi wanda shima irin wannan na yan 419 dinne idan kuka duba xakuga kome kamar yadda na gaya muka www.freemtnawoof.tk
Www.freemtnawoof.tk.
Sabo da haka yan,uwa ku lura dakyau da xarar kunga wata garabasa kada kuna saurin gwadawa kuna tambaya akan irin wannan domin matambayi baya bada idan har kuna yan tambaya akan irin wadannan matsalolin to Insha Allah yan 419 baxasuyi nasara akan muba,
Domin karin bayani saiku biyomu ta wannan number 08169872309
Note: idan ka karanta dan Allah kayi kokarin turashi xuwa wani gun kamar su facebook whatsapp instangram tweatter 2go da dauransu, domin yin hakan xai taimakemu sannan xamu gujewa fadawa sharrin yan 419 sabo da haka dan Allah inka karanta ka daure ka turashi wa ko ina ta yadda alumma xasu amfana,
.
Allah ya kiyayemu ya karemu daga aikata irin wadannan aiyukan masuyi sukuma Allah ya shiryesu ameen
COMMENTS