Kamar de yanda kuka sani akwai hanyoyi masu yawa da akebi domin fita daga tsarukan mtn na daukan kudi to saide wasu hanyoyin koda ka fita ba...
Kamar de yanda kuka sani akwai hanyoyi masu yawa da akebi domin fita daga tsarukan mtn na daukan kudi to saide wasu hanyoyin koda ka fita bazasu denaba domin kuwa wata hanyar ba daya bace da wata ko wanne tsarin cire kudi akwai hanyar fitarsa, to shi wannan post nawa zai koyar dakai yanda zakaga duk tsarukan da kake ciki wanda ta dalilinsu ake cirema kudi, haka zalika wasu lokutan har kiran custormer care ake domin su fitar da mutum to amma hakan saiya gagara saide kaji sun baka wasu lambobi suce ka danna to kuma koda ka danna wannan lambobin wani lokacin sai kaga ba,ayi daceba, to yanzude ga yanda zakuyi
.
Da farko ku danna *447# bayan kun danna wannan lambobi zakuga sun nuno muku wasu Rubutu to kawai kuyi Replay da number 7 sannan ku sake Replay da number 3 sannan ku sake Replay da 1 shikkenan da zarar kunyi haka zakuga sun nuno muku dukkan tsarukan da kuke ciki to wannan tsarukan da kukaga gani sabo dasu ake cire muku kudi dan haka domin fita daga dukkan tsarukan saiku dinga bi kuna Replay da number da tsarukan suke ciki misali idan kuna 1 mtn collertune to sai kuyi Replay da 1 haka sauranma duk da lambobinsu zakuyi Replay, da zarar kun gama shikkenan kun fita insha Allah,
.
Allah ya bada sa,a
COMMENTS