kamar de yanda ka sani wani lokacin haka kawai yayin daka dora memory card dinka a wayar android sai kaga yaki hawa saide ya Rubutoma memory...
kamar de yanda ka sani wani lokacin haka kawai yayin daka dora memory card dinka a wayar android sai kaga yaki hawa saide ya Rubutoma memory damage da zarar ka danna saiya Rubutoma format to da zarar ka amince shikkenan saide kayi format dinsa domin kuwa babu yanda za,ayi memory dinnan yahau a wannan android din inde ba format din aka yiba
.
To Alhamdulillah yanzu ga hanyar da zakabi domin ka gyara wannan matsalar ta memory damage.
Idan memory dinka ya samu irin wannan matsalar to ka fitarshi daga wayar taka saika nemi wata wayar kamar symbian ko java sannan kayi download a google na BlueFtp.jar idan kuma symbian ce kawai kayi download na explore idan kuma kana da ita shikkenan to bayan ka nemi wannan app din sai kayi install dinsa sannan saika budeta kaje kan memory din naka zakaga ya hau to abin da zakayi anan shine, ka duba foldar din memory din zakaga bakin foldodo wato foldodin da babusu, to abin da zakayi anan saika dinga bi kana goge kowace folder wanda kasan bata da amfani sannan ka dinga buda wasu foldodin acikinsu akwai virus shima duk sai kabi ka dinga gogesu. Har saika tabbata babusu, to da zarar ka kammala gogewa duk wani tarkace, to yanzu kawai saika fidda memory daga wannan javar ko symbian din, yanzu saika dorashi akan android din taka shikkenan, nan take zakaga yahau insha Allah
.
COMMENTS