Daya daga cikin manyan jami'oi da ke kasar Zambia ta yi kira ga dalibai mata a kan su daina zuwa dakin karatu (laburari) sanye da tufafi...
Daya daga cikin manyan jami'oi da ke kasar
Zambia ta yi kira ga dalibai mata a kan su
daina zuwa dakin karatu (laburari) sanye da
tufafin da basu dace ba saboda hakan na jan
hankalin dalibai maza. Jami'ar University of Zambia da ke Lusaka, babban
birnin kasar, ta lika takardu a wurare da ke kusa da
dakin karatu, inda ta fada musu su rika sa tufafin
da ba zai nuna tsiraicinsu ba. Al'adar mutanen Zambia wadda ta ke yankin
kudacin Afirka ta masu tsatssauran ra'ayin al'ada
ce. Sai dai daliban jami'ar sun fi son su yi shiga irinta
'yan zamani a cewar wakilin BBC a kasar Kennedy
Gondwe . "Mun lura da cewa akwai wasu dalibai mata da ke
yin shigar da ke nuna tsiraicinsu idan sun je dakin
karatu, kuma al'amari ne da ke damun dalibai
maza", a cewar sanarwar. "Akan haka muna kira ga dalibai mata da su rika
yin shigar da ba za ta nuna tsiraicinsu ba yayinda
suke amfani da kayan jami'a." Sai dai wasu mata sun nuna rashin amincewarsa
kan umarnin da hukumomin jami'ar suka bayar. "Idan kun je wurin ne domin ku yi karatu shin me
ya sa ku ke kallon kafafuwan mata ?" in ji Dikina
Muzeya wadda daliba ce a jami'ar. "Ku maida hankali a kan litattafanku kawai," a
cewarta. Sai dai Killion Phiri wanda shi ma dalibi ne a jami'ar
ya goyi bayan matakin. "Ya ce ka san yadda halittar jikin mata take, tana sa
sha'awa," kamar yadda ya shaida wa BBC. "Ta ya za a yi ka maida hankali wajan karatu idan
wata ta saka gajeran siket ko rigar da ta kama
jikinta? Za ka fara tunanin wasu abubuwa kuma ba
za ka iya karatu ba".
.
Source @bbc hausa
COMMENTS