Tsohon Gwamnan Jigawa Alhaji Sule Lamido na cikin manyan 'yan siyasar Najeriya da suka bayyana aniyar tsayawa takarar shugaban kasa a ja...
Tsohon Gwamnan Jigawa Alhaji Sule Lamido na
cikin manyan 'yan siyasar Najeriya da suka
bayyana aniyar tsayawa takarar shugaban
kasa a jam'iyyar adawa ta PDP a zaben 2019. Sai dai kuma ana ganin jam'iyyar PDP da tsohon
gwamnan zai nemi ta tsayar da shi, ba za ta yi
sakaci ba wajen zaben tumun-dare a matsayin dan
takararta, a yunkurin da take na kwace mulki daga
hannun APC. A shekarar 2015 ne Shugaba Muhammadu Buhari
ya kayar da Goodluck Jonathan na PDP, kuma tun
daga lokacin ne jam'iyyar ke ta fadi-tashin ganin ta
farfado. A don haka babban kalubalen da ke
gaban PDP shi ne tsayar da dan takarar da zai
kawar da gwamnatin APC ta shugaba Buhari a zaben 2019. Za mu rinka yin nazari kan kalubalen da masu
neman takarar shugabancin kasar za su iya
fuskanta, inda a wannan karon muka duba
muhimman abubuwa biyar da za su iya zama
barazana ga takarar Sule Lamido a jam'iyyar ta PDP: 1. Yana fuskantar shari'a Alhaji Sule Lamido na fuskantar shari'a kan zargin
almundahana da kudaden al'umma a lokacin da
yana gwamnan Jigawa. A 2015 ne Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa
ta EFCC ta gurfanar da shi a kotu da wasu 'ya'yansa
biyu kan laifuka 27 da suka kunshi sama da fadi da
kudaden jama'a. Ko da yake tsohon gwamnan ya musanta
dukkanin zarge-zargen da ake ma sa, kuma har
yanzu kotu ba ta kai ga yanke hukunci kan shari'ar
ba. Amma wasu masu sharhi na ganin wannan zai iya
zama matsala ga aniyar Sule Lamido ta samun tikitin
jam'iyyar PDP. Suna ganin PDP ba za ta yarda ta tsayar da dan
takarar da za ta zo tana kokarijn kare wa ba,
musamman ganin cewa ba a san yadda shari'ar za
ta kaya ba. Jam'iyyar za ta nemi ta tsayar da dan takarar da ba
ya da wani kalubale a kotu, domin kada 'yan
adawa su yi amfani da wannan damar su bata
tafiyar jam'iyyar, musamman ganin yadda batun cin
hanci da rashawa ya taka rawa a zaben 2015
wanda jam'iyyar ta sha kaye. 2. Ra'ayin kansa Masharhanta siyasar Najeriya na kallon Sule Lamido
a matsayin mutum da ke da ra'ayin kansa. Kuma ba
kasafai ake iya tursasa shi ba. Suna ganinsa a matsayin mutum da yake nuna isa,
musamman yadda yake nuna ba ya da wani uban
gida da zai iya yi masa hanzari. Wasu kan yi amfani da yadda rayuwa ta kasance
tsakaninsa da tsohon mai gidansa marigayi
Abubakar Rimi, wurin nuna cewa yana da nuna isa. Amma daga bisani tsohon gwamnan ya sasanta da
mai gidan nasa, kuma ya bayyana Rimi a matsayin
wani jigo na siyasa a Najeriya. Sai dai wasu na ganin za a iya cewa Olesegun
Obasanjo unban-gidansa ne kuma yana fada masa
ya ji. Ita dai jam'iyyar PDP za ta so ta tsayar da dan
takarar da za ta iya tankwasawa, tare da mutunta
bukatunta, musamman ganin halin da ta smau
kanta a ciki. Masu neman takara a PDP Alhaji Atiku Abubakar Ayo Fayose Malam Ibrahim Shekarau Sule Lamido Ahmed Makarfi (bai bayyana ba kawo yanzu) 3. Karbuwa a Arewa Ganin yadda Shugaba Muhammadu Buhari ke da
magoya baya a arewacin Najeriya, PDP za ta so ta
tsayar da dan takarar da zai iya ja da shugaban. Sule Lamido, yana cikin manyan 'yan adawa da ke
sukar gwamnatin Shugaba Buhari da jam'iyyar APC. Amma wasu na ganin a matsayinsa na gogaggen
dan siyasa a Najeriya, yana iya adawa da Buhari
amma ta hanyar da tsohon gwamnan zai samu
farin jinin jama'a. Kamar yadda wasu suka bada misali da irin
mamayar da Donald Trump ya yi a Amurka wajen
sukar gwamnati ta hanyar da mutane suke so. Yadda tsohon gwamnan yake adawa da Buhari,
wasu na ganin ya kara jawo masa bakin jini a
tsakanin wasu 'yan arewar. Duk da ana ganin farin jinin Shugaba Buhari ya
ragu a arewa amma wasu na ganin Sule Lamido ba
ya da karbuwar da har zai iya ja da shi. PDP za ta yi kokarin tsayar da dan takarar da zai yi
gogayya da Buhari wanda zai wawuri wasu daga
cikin kuri'un da shugaban ya samu a 2015. Masu sharhi na ganin duk dan takarar da zai ka da
Buhari, to wajibi ne ya samu kuri'u masu gwabi a
arewa. Wane ne Sule Lamido An haife shi a shekarar 1948 a garin Bamaina,
Karamar Hukumar Birnin Kudu a Jigawa Shekararsa 69 Tsohon dalibin Barewa College ne Tun yana matashi ya ke siyasa An zabe shi dan majalisa a jamhuriya ta biyu a
karkashin jam'iyyar PRP Yana cikin mutanen farko da suka kafa
jam'iyyar PDP Ya kasance Ministan harkokin wajen Najeriya
daga 1999-2003 Ya kasance Gwamnan Jigawa daga 2007 zuwa
2015 An taba daure shi a zamanin mulkin Janar Sani
Abacha EFCC ta gurfanar da shi Kotu kan zargin halatta
kudaden haram, zargin da ya musanta 4. Alakarsa da gwamnoni Jam'iyyar PDP na kokarin farfado da martabarta ga
'yan Najeriya ne a yanzu bayan ta sha kaye a zaben
2015 bayan shafe shekara 16 tana mulki, lamarin
da ya so ruguza jam'iyyar. Wasu na ganin gwamnonin PDP ne za su kasance
alkiblar jam'iyyar, musamman wajen zaben dan
takarar shugaban kasa a babban taronta na kasa. Kuma duk wanda jam'iyyar za ta tsayar dole sai ya
samu karbuwa da goyon bayan gwamnonin
jam'iyyar. Amma masharhanta na ganin alakar tsohon
gwamnan na Jigawa da gwamnonin PDP tana da
rauni, saboda ba ya kan mulki yanzu, kuma
yawancin gwamnonin ba 'yan arewa ba ne. Haka ma alakarsa da Tsohon Shugaban kasa
Goodluck Jonathan ba tada kyau sosai. Kuma ana
ganin har yanzu Mr Jonathan na da karfi a
jam'iyyar. Gwamnan jihar Gombe Ibrahim Dankwambo duk
da bai fito ya bayyana aniyarsa ba ta tsayawa
takarar shugaban kasa, amma ana ganin idan har
ya fito ya nuna yana so, to gwamnonin PDP na iya
mara ma shi baya. 5. Karfin Iko Kwace mulki daga jam'iyyar APC mai mulki shi ne
babban kalubalen jam'iyyar PDP. Jam'iyyar adawar ta Najeriya za ta so ta tsayar da
dan takara mai kudi da karfin fada aji, wato dan
takarar da ke rike da wani madafin iko. Za ta so ta tsayar da dan takarar da zai iya tallafawa
sauran 'yan takararta da kuma jam'iyyar domin
yakar APC a zaben gwamnoni, 'yan majalisa da na
shugaban kasa. Hidimar daukar nauyin wakilan jam'iyya a babban
taron fitar da dan takara, harka ce da ke bukatar
kudi, kuma hakan zai yi tasiri ga zaben dan takarar
jam'iyyar. Masana siyasa na ganin PDP ba za ta so ta tsayar da
wanda za ta sha wahala da shi ba musamman
wajen yakin neman zabe da hidimar magoya baya. Ana ganin Sule Lamido ba shi da karfin yin hakan,
musamman ganin ba ya rike da wani mukami
yanzu. Kuma za a cewa zai fuskanci kalubale wurin
nemo gudummawa da jan hankalin masu hannu
da shuni.
.
Copyright @bbchausa
COMMENTS