Fadar shugaban Najeriya ta yi zargin cewa makiya na kokarin bata sunan Shugaba Muhammadu Buhari domin ganin ya fadi a zaben 2019. Mai magana...
Fadar shugaban Najeriya ta yi zargin cewa
makiya na kokarin bata sunan Shugaba
Muhammadu Buhari domin ganin ya fadi a
zaben 2019. Mai magana da yawun shugaban Femi Adesina, ya
ce wasu mutane na sauya ma'anar kalaman
shugaban da jirkita su domin cimma manufar
siyasa. Mr Adesina na mayar da martani ne kan korafe-
korafen da ake yi ne kan jinyar da shugaban ke
zuwa Ingila. A ranar Talata ne Shugaba Buhari, mai shekara 74,
ya sake komawa Ingila domin ganin likitocinsa -
wannan ne karo na hudu da shugaban ke tafiya
jinya Landan. A watan Agustan bara ne ya koma kasar bayan
shafe wata uku yana jinya a Ingila. 'Yan kasar da dama dai na cigaba da sukar wannan
matakin, suna masu cewa kamata ya yi shugaban
ya mayar da hankali wurin gyara fannin lafiya na
kasar. Wasu sun bayar da misalin wasu kalamai da aka ce
Shugaba Buhari ya yi a baya, inda ya soki yadda
ake tafiya ganin likita a kasashen waje, amma sai
ga shi shi ma ya zo yana yin hakan. Sai dai Femi Adesina ya ce ana sauya wa kamalan
shugaban ma'ana ne. "Da farko suna mayar da hankali ne wurin sauya
wa kalamansa ma'ana, amma da suka ga hakan ba
ya tasiri,... a yanzu sun koma kirkirar karya da
hanyar amfani da shafukan sada zumunta," a
cewarsa. Adesina ya bayar da misali ga jawabin da Buhari ya
yi a shekarar 2015 lokacin yana dan takara a
Chatham House, a Landan, inda ya ce "an sauya"
wasu kalmomi daga cikin jawabin domin nuna
cewa shugaban ya ce "bai ga dalilin fita waje
neman magani ba bayan akwai likitoci a Najeriya". Ya kara da cewa amma Allah ya sa cikakken
jawabin da shugaban ya yi na nan a bayyane
kamar yadda aka wallafa a wancan lokacin. Wannan batu na rashin lafiyar Shugaba Buhari ya
dade yana haifar da ce-ce-ku-ce a kasar,
musamman ganin cewa ya tafi Landan din ne a
lokacin da ma'aikatan lafiya a kasar ke yajin aiki. Ma'aikatan na zargin gwamnati da kasa biya musu
bukatunsu da suka hada da inganta harkokin
lafiya a kasar ta hanyar samar da kayan aiki. Sai dai
gwamnatin ta ce tana iya kokarinta. A kwanan baya ne Shugaba Buhari ya sanar da
aniyarsa ta neman wa'adi na biyu a zaben kasar da
za a yi a badi. Sai dai wasu na kara nuna shakku kan koshin
lafiyarsa musamman bayan da ya sake tafiya
Landan ganin likita. Wannan shi ne karo na biyu a cikin mako guda da
zai ga likita bayan da ya gana da likitocin nasa a
kan hanyarsa ta dawowa daga Amurka a makon
da ya gabata.
.
Source @bbc hausa
COMMENTS