Aure babban ni’ima ne a rayuwa. Aure alama ce ta cikar Dan Adam. Aure shi ne silar yaduwar al’umma. Sannan uwa uba Sunnar Ma’aiki (SAW). Ina...
Aure babban ni’ima ne a rayuwa. Aure alama ce
ta cikar Dan Adam. Aure shi ne silar yaduwar
al’umma. Sannan uwa uba Sunnar Ma’aiki (SAW).
Ina samari masu neman aure? Ga shawarwari
gare ku: Da farko dai kafin ka fara neman aure, kamata
yayi ka sami natsuwa kuma ka nemi yarinyar
kirki, ko a cikin ‘yammata nagari ka nisanci guda
3, su ne kamar haka: (1). Tagari ce amma ba ta sonka (2). Uwarta ba ta da tarbiyar muslunci ko kadan (3) Uwar ita ma ta gari ce amma tana nuna maka
matsananciyar adawa Sannan idan ka tashi neman aure ka sani cewa,
ko motar da take karfe wacce za ka rika hawa ta
kai ka duk inda ka keso a lokacin da kake so,
dole sai ka samo lafiyayyiya sannan ka koyi
yadda ake sarrafa ta, da yadda za ka lallaba ta har
ta jima maka sosai. Dole ka rika kula da ita wajen kwalliyarta da gyaran injinta lokaci zuwa lokaci
gwargwadon yadda wanda yayi ta ya tsara, kana
wanke ta kuma kana ba ta irin man da take sha
wanda zai gyara injinta. Kuma in ka tashi yin
tafiya ba ka kure maleji ba, bare ta makale maka a
cikin daji ko ta saka ka yi hatsari da sauransu. To haka mace take, idan ka aura kai ma dole ka
mike da yin wasu hidimomi matukar kana da
bukatar ganin lafiyarta da kwanciyar hankalinka,
da zama mai dorewa. Mace za ta rika yi maka
hidima, amma kai ma maigida na kwarai akwai
naka irin hidimar. Shin ka auro wacce take sonka ? Idan hark a yi dace ka auri mata tana sonka
komai ka ke so za ka samu. Sannan ka zabo mai
tarbiyya mai sanin addini da kama kai, mai kunya,
bayan haka sai ka fara dora ta a kan hanyar da
kai kake bukata, ta tafi a kanta. Amma ka fahimci abu guda daya. Mace har
kullum tana hukunci da zuciyarta ne, tana da
tausayi da soyayya da daukan abu mai hatsari a
matsayin karamin abu. Duk lokacin da zuciyarta
ta baci za ta iya yin komai ba tare da tunanin abin
da zai kai ya komo ba. Saboda dogaron da ta yi a kan zuciyarta, shi ya sa komai ilimin mace idan
ranta ya baci ko kuma aka yi mata auren dole za
ta iya yin komi. Kenan idan ka auri wace ba ta
sonka don Allah ka yi mata uzuri. Ka yi kokari
kaunarka ta shiga zuciyarta sannan ka nemi
hakkokinka. Maigida na kwarai muna yi maka zaton aiki da
kwakwalwa sama da zuciyarka, kana da
karancin nuna soyayya, da tausayi, ba kamar
matarka ba, to amma kwakwalwarka takan nuna
maka me ya dace ka yi? Miji na kwarai ne wanda ya san darajar mace,
yake ba ta hakokinta, idan mace ta yi aiki da
zuciyarta to lallai shi kuma sai ya yi aiki da
kwakwalwarsa. Amma ya dauki mace kamar abin
hawa kullum sai dai ya yi amfani da ita ba wani
kulawa da ita, gaskiya akwai matsala. Yanzu ya za a yi ka zama maigida na kwarai
bayan ba ka kulawa da matarka? Ka nemi taimakon Allah (SWT) wajan samun mace
ta kwarai, mai saukin kai wacce zata tafi dai-dai
da bukatarka, sannan ka nemi wacce take son
ka, ka zabo mai addini mai son muslunci, ka auro
‘yar namiji ba ‘yar mace ba. Sauran kuma ka
baiwa Allah (SWT) ikonsa. Bayan nan ka shirya cewa zaka rika ganin abubuwan da baka so,
amma haka Allah yayi ta dole sai kayi hakuri.
karka taba saukowa dai-dai da matsayinta, sai
gidanka ya lalace. kullum ka rika cewa ita mace
ce kai kuwa namijine to sai a zauna lafiya. Allah (SWT) ya bamu mata nagari, suma matan
Allah ya basu maza nagari. Amin
.
Source: @leadershipayau
COMMENTS