Blog Archive

Powered by Blogger.

Ya Zanyi Idan Mijina Ba Ya Iya Biya Min Bukata?

’Yan uwana mata barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan fili namu mai matukar farin jinni, wato SIRRIN IYAYEN GIJI… a jaridarku ta LEAD...



’Yan uwana mata barkanmu da sake saduwa da
ku a cikin wannan fili namu mai matukar farin
jinni, wato SIRRIN IYAYEN GIJI… a jaridarku ta LEADERSHIP A YAU LAHADI. Kamar yadda ku ka sani, shi wannan shiri a na
yin shi ne, don matan aure zalla, domin ba su
shawarwari ta kowane bangare na rayuwarsu ta
yadda za su samu su gyara zamantakewarsu da
mazajensu da mu’amalarsu ta bangaren girki,
tsafta, gyaran gida da gyaran jiki, irin abubuwan da su ka kamata mu mata mu dinga ci domin
karin ni’imarmu da gamsuwar mazajenmu da ma
duk wani abu da ya shafi rayuwar ’ya mace. Da fatan za ku dinga bibiya ta a cikin wannan
shafi. Gurin da na yi kuskure, sai na ce Ina neman
afuwar ubangiji da afuwarku, domin ajizanci irin
na dan adamtaka, gurin kuma da na yi daidai sai
na ce Allah Ya hada mu a ladan bakidaya. A wannan makon zan amsa tambayoyin da wasu
daga cikin masu karatu su ka aiko ne. Bismillah: Tambaya: Assalamu alaikum. Anty Baby, tambayata a nan ita ce, ni mijina ba ya biya min bukata a shimfida. Ma’ana; ta wajen jima’I; mu na fara saduwa idan ya samu biyan bukatar kansa shikenan sai ya daga ni ko da kuwa ban ji dadi ba. Ba ruwansa da sha’awar da zan kasance a ciki kuma ba ruwansa da damuwar da zan yi. Shi kansa kawai ya sani. Haka ma gobe idan ya zo zai kuma yi. Abin nan ya na matukar damu na har na ji na fara tsanar sa a raina. Meye shawararki, Anty Baby? Amsa: ’Yar uwa ya na daga ilimin da ya kamata a
dinga sanar da mutanen da su ka mallaki
hankalin kansu shi ne ilimin jima’i a Musulunci.
Manzon Allah (saw) ya ce, kada dayanku ya afka
wa matarsa, kamar yadda jaki ya ke afkawa jaka.
Idan dayanku zai je wa iyalinsa, ya kamata ya aika dan aike, wato ya kamata a ce kafin ya
kwanta da matarsa su gabatar da duk wani wasa
da zai motsa musu sha’awa, domin samun
gamsuwar su kansu ma’auratan. Sannan idan
mutum ya sadu da matarsa, bai kamata ya yi
gaggawar fitar da gabansa daga cikin matucinta ba har sai wannan matar ta sami gamsuwa daga
gare shi, saboda wata matar ba ta samun
gamsuwa a daidai lokacin da shi mijin ya sami
gansuwa, har sai ya jira ita ma matar ta sami tata
gamsuwar. Wani mutumin ba ruwansa; da zarar ya sami
gamsuwa da matarsa koda a iya wasan da su ke
yi ne, to fa shi ya gama, ba ruwansa da ita. Shi ba
abinsa ya yi ma sa zafi. Kun ga wannan shi ne
karshen rashin adalci. Wata matar kuma ta na da
doguwar sha’awa, saboda haka, idan mijinta bai yi wasa da ita ba, sannnn bai jira ta samu
gamsuwa daga gare shi ba, to maniyyin da ya ke
jikinta ba zai sauko ya hadu da nasa ba, sai dai ya
tsaya ma ta a mararta. Daga nan kuma sai ciwon
mara, sai ciwon ciki, sai ciwon kai, sai warin gaba.
Daga nan sai mace ta dinga tsintar kanta da rashun kuzari da rashin walwala. Ta rasa abin da
ya ke yi ma ta dadi, kuma wannan ke sa mace ta
dinga jin haushin mijin da tsanar mijin. Sai ka ga
mace ba ta girmama miji yadda ya kamata. A rasa
dalili. Nan kuwa rashin ba ta hakkinta a shimfida
ne ya jawo ma sa. Sannan ya kamata mu sani cewar mata kala-kala
ne kamar yadda maza su ke kala-kala. Akwai mai
karfin sha’awa, wacce idan ba ta sami daidai ita
ba, akwai damuwa. Sai dai ka ga auren ya na kai
kawo. Karshe dai sai an rabu hankalinta zai
kwanta. Ba yin ta ba ne; haka Allah Ya yi ta. Haka su ma mazan, wani idan ya sami wata matar, da
kanta za ta gudu. A-yi-a-yi ta dawo, ba za ta
dawo ba, amma wata ta na kokari ta sanar da
’yan gidansu cewar ya fi karfinta. Shawara ga mata da mazan da ba sa iya biya wa
junan bukata; su sani ba sai ta kai su ga rabuwa
ba. Idan ka san ba ka da juriyar da za ka iya biya
wa matar ka bukata a shimfida ba, to ka dinga
wasanni da ita sosai kafin ka shige ta, kuma ka
tabbatar ka gane guraren da idan ka tattaba ma ta ta ke jin dadi sosai yadda kafin ku zo saduwa
ka gama tayar ma ta da sha’awarta, ta fara jin
dadi sosai. Ka ga ka na shigar ta, kafin ka biya
bukatarka, ta gama jin dadinta. Za ka ji ta sharkaf;
komai ya yi daidai. Shawara ta biyu; ka kasance
mai neman maganin karin karfin mazakuta da darin kuzari yadda matar taka za ta ji ka gagau. Uwar gida idan mijinki ya na fama da rashin
karfin mazakuta ko ba ya biya miki bukatarki a
shimfida sai ki yi ma sa wannan hadin, ki samu: Bakin gagai Jan gagai Namijin goro Tsintsiyar maza Tatarida ’Ya’yan Dabino Citta mai yatsu Masoro Barkono A hade, a dake su a tankade lukwui a dinga zuba
ma sa a farfesu ko gasashshen nama ya na ci ko
ki tafasa ma sa ki sa zuma ya dinga sha kamar
shayi. Tambaya: Anty Baby, mene ne maganin warin baki da yadda zan magance shi? Amsa: A abubuwan da ke janyo warin baki akwai
rashin wanke baki bayan an ci abinci, domin a
yadda a ke so, duk sa’adda mutum ya ci abinci da
dare ne ko rana a na bukatar ya wanke bakinsa.
Babu shakka duk yadda bakin mutum ya ke da
tsafta, to idan ya ci abinci ya bar bakin tsawon awa guda bai wanke ba, to fa kwayoyin cuta ne
za su taru, don su cinye guntun abincin ciki. Idan
sun gama kuma su fara cin hakora. Daga nan sai
bakin mutum ya rika wari. Sannan da yawa daga
cikin mutane sun dauka wanke baki sai an tashi
daga barci ne kawai, tunda a lokacin ne ake jin bakin ba dadi. To, bincike ya nuna wanke baki da
dare kafin kwanciya ya fi amfani fiye da
wankewa da safe. Shawarar da zan ba ki a nan ita ce, ki nemi man
kanumfari ka rika wanke baki da shi sau uku a
rana, haka ma duk lokacin da ki ka ci abinci ki
nemi ruwa ki wanke bakinki, sannan ki nemi citta
ki rika tauna ta a lokacin da za ki yi barci tsawon
kwana bakwai. Haka kuma ki nemi gawayi ki dandaka shi, ki hada shi da gishiri ki rika wanke
baki da shi ko sau biyu a rana. Sannan shi kansa
gawayin a na tauna shi da hakori a tsotse
ruwansa, don ya na maganin warin baki. Haka a na zuba danyen wake guda uku a abi a
tauna a tsotse ruwan a zubar da tukar. Hakan ya
na maganin warin baki. Bayan nan ki nemi Apple
Sider Benger ki rika shan cokali uku a lokacin da
za ki yi bacci. Haka a na watsa kanumfari guda uku ko sama da
haka a baki a dinga tsotsa. Ya na kawar da warin
baki kuma ya na saka kamshin jiki. In sha Allahu
idan ka bi wadannan hanyoyi za ka samu waraka
da yardar Allah. ’Yan uwana mata, baki ya na taka rawa wajen
mu’amalar soyayya a wajen mijinki; kar ki bari
mijinki ya zo zai sumbace ki ya ji bakinki ya yi ba
dadi. Ki kasan ce mai kula da bakinki yadda duk
sanda angonki ya so ku hada baki, domin ku ji
dadin rayuwa; ya ji daddadan kamshi na fitowa daga bakinki. Amman idan ki ka bari ya ji banki
ya na wari, za ki fita daga ransa. Take sha’awarsa
za ta dauke daga kanki, kuma zai ji ya fara tsanar
ki. Bari na bar ku haka, sai wani makon idan Allah
ya kai mu
.
Source: @leadershipayau

COMMENTS

Name

Al'ajabi,13,Android zone,69,Applications,3,Aure,25,Blogger zone,1,computer zone,4,Dadin Kowa sabon salo,27,Facebook zone,12,Free Browsing,2,Hausa Films,1,Hausa novels,1,hotuna,2,Java zone,15,Kannywood,55,kiwon lafiya,35,Mata,12,Musics,24,Network,21,News,146,others,16,siyasa,81,Soyayya,3,Symbian zone,5,Video clips,33,video tutorials,3,Whatsapp,1,
ltr
item
Ameer: Ya Zanyi Idan Mijina Ba Ya Iya Biya Min Bukata?
Ya Zanyi Idan Mijina Ba Ya Iya Biya Min Bukata?
http://fm.nextwapblog.com/files/6475/sirrin-mace.jpg
Ameer
https://ameeryau.blogspot.com/2018/05/ya-zanyi-idan-mijina-ba-ya-iya-biya-min.html
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/2018/05/ya-zanyi-idan-mijina-ba-ya-iya-biya-min.html
true
2994989324915487916
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy