Jami'an da ke kula da namun daji a Uganda na farautar wata damisa da ta kwace wani karamin yaro mai shekaru uku kuma ta cinye shi a dare...
Jami'an da ke kula da namun daji a Uganda na farautar wata damisa da ta kwace wani
karamin yaro mai shekaru uku kuma ta cinye
shi a daren ranar Juma'a. Yaron dai da ne ga daya daga cikin ma'aikata da ke
aiki a wurin kula da namun daji na Queen Elizabeth
National Park da ke kasar Uganda. Elisha Nabugyere ya bi mai renonsa waje a
bangaren rukunin gidajen ma'aikata da ba a
katange ba lokacin da damisar ta far masa, a cewar
kamfanin dillancin labarai na Reuters. "Mai renon nasa ba ta san cewa yaron na binta a
baya ba. Ta ji lokacin da ya yi ihu amma duk da
cewa ta yi kokarin ceto shi daga hannun damisar
amma hakarta bata cimma ruwa ba. Damisar ta wuce da shi cikin daji, kuma an tura da
wasu cikin daji domin kubutar da yaron amma sai
washegari suka gano kwarangwal din kansa,"a
cewar kakakin hukumar kula da namun daji ta
Uganda Bashiir Hangi. "Ana kan farautar damisar domin a cafketa kuma a
cireta daga sauran namun daji saboda muddin ta
fara cin naman bil'dama, to za ta iya sake neman
wani mutumin da za ta hallaka, a don haka tana da
hadari sosai" in ji shi
.
Source by @bbchausa
COMMENTS