'Yan Najeriya kalilan ne suka yarda da 'yan sanda, amma an ware daya daga cikinsu a matsayin "wanda ya fi kin karbar na-goro ko...
'Yan Najeriya kalilan ne suka yarda da 'yan
sanda, amma an ware daya daga cikinsu a
matsayin "wanda ya fi kin karbar na-goro ko
cin hanci" a kasar An bayyana Adekunle Rufus Adedeji, wanda
jami'in 'yan sanda ne da ke aiki a fannin binciken
laifuka a jihar Ekiti, a matsayin dan sandan da bai
taba karbar cin hanci ba. Wani binciken da kungiyar kare hakkin bil'adama
ta Constitutional Rights Awareness and Liberty
Initiative ta yi ne ya bayyana shi a matsayin dan
sandan da ya fi gaskiya a kasar. Kwanan nan ne kuma ofishin jakadancin Amurka a
Najeriya ya ba shi kyautar "Dan sandan da ya fi
dagewa a aiki a kasar". 'Yan sandan Najeriya sun yi kaurin suna wurin
karbar cin hanci da kuma take hakkin bil'adama,
zargin da hukumominsu suka sha musanta wa. Dan sandan ya shaida wa shashen Yarbanci na BBC
a wajen wani biki cewar yakan ji kunya a lokacin
da 'yan Najeriya ke ci gaba da kaskantar da 'yan
sanda, yana mai cewa bai kamata a daura wa
hukumar 'yan sanda alhakin kasa aiki yadda ya
kamata ba. Ya ce: "Da gaske akwai miyagu a cikin 'yan sanda,
amma halayyar dan sanda ta danganta ne da
yadda aka tarbiyyantar da shi a gida. Wannan na
nuna dabi'ar al'umma ne gaba daya." Ya kara da cewa gwamnati ce ke da alhakin abin da
'yan sanda suka zama. Saboda haka, sai ya yi kira ga gwamnati da ta bayar
da kudi domin kyautata jin dadin 'yan sanda a duk
fadin kasar. Ya ce idan dan sanda ba shi da yakinin cewar za a
biya masa bukata, zai iya neman wata hanya ta
daban domin biyan bukatarsa. Sai dai kuma ya ce duk da haka bai dace jam'in 'yan
sanda ya karbi nagoro ko kuma ya tauye hakkin
bil'adama ba.
.
Source @bbc hausa
COMMENTS