Aamir Khan Jarumi Aamir Khan na daga cikin jaruman fina- finan Indiya da suka samu damar sauke faralli, wato aikin Hajj. Aamir Khan dai ya s...

Aamir Khan Jarumi Aamir Khan na daga cikin jaruman fina-
finan Indiya da suka samu damar sauke faralli, wato aikin Hajj. Aamir Khan dai ya sauke faralli ne a shekarar 2012
tare da mahaifiyarsa Zainat Hussain. Aamir Khan dai ya jima da yi wa mahaifiyarsa
alkawarin cewa za su kai ta Makka ta sauke faralli,
to hakan ya sa ya cika alkawarin da ya dauka, suka
tafi tare suka sauke faralli. Don haka a iya kiran Aamir Khan da Alhaji a
hausance ke nan. Aamir Khan dai fitaccen jarumi ne da ya fito a
manyan fina-finan Indiya da suka shahara ciki har
da Laagan da 3 Idiots da Ghajini da kuma Tare
Zameen Par.
.
AR Rehman
AR Rehman, fitaccen mawaki ne kuma mai kida a fina-finan Bollywood. AR Rehman ya yi aikin Hajj har sau biyu, na farko a
shekarar 2004, sannan bayan shekara biyu kuma
wato a 2006, ya sake komawa. AR Rehman, a cikin wata hira da ya yi da manema
labarai a Indiya, ya ce yana mai matukar alfahari da
kasancewarsa Alhaji. Ya ce ya cika babban burin rayuwarsa da ya ziyarci
kasa mai tsarki inda ya yi Umrah da aikin Hajj. Wasu daga cikin wakokin da AR Rehman ya yi
akwai Maa Tujhe Salam da wakar Muqabla da kuma
wakar Dil Se Re.
.
Kader Khan
Kader Khan tsohon jarumin fina-finan Indiya ne da ya shahara wajen barkwanci. Ya fito a fina-finai sama da 300. Ya fara fitowa a fim ne a shekarar 1973 a fim din
Daag. Mafi yawancin fina-finansa na barkwanci ne. Kader
Khan ya kan rubuta labarin fim ma. Daga cikin fina-finan da ya fito akwai Judaai da
Hero No. 1 da kuma Judwaa. A shekarar 2014 ne Kader Khan ya yi aikin Hajj tare
da 'ya'yansa maza biyu wato Shahnawaz da
Sarfaraz. Dilip Kumar Dattijon jarumi, wanda har yanzu ba a yi kamarsa a Bollywood ba. Cikakken sunansa Muhammed Yusuf Khan, yanzu yana da sama da shekara sama da 90 a duniya. Shi ne jarumin da ya fi duk jarumai maza na Indiya samun lambobin yabo. Ya taka muhimmiyar rawa a Bollywood. Ba jarumi kadai ba, ya kan rubuta labarin fim, kuma
mai fafutuka ne. Shima ya sauke faralli, amma sai da ya fara zuwa
Umrah a 2013, da shekara ta zagayo wato a 2014,
sai suka tafi aikin Hajj tare da matarsa Saira Banu. Daga cikin fina-finan Dilip Kumar akwai Gunga
Jumna da Kranti da Saudagar da kuma Mashaal.
.
Muhammad Rafi
Mohammad Rafi, Fitaccen mawaki ne a Indiya. Ya yi wakoki sama da dubu 28 daga tsakanin
shekarar 1944 zuwa 1980. Daga cikin wakokinsa da suka yi fice akwai wakar
Kya Hua Tera Wada da Mere Mehboob Tujhe Salam
da kuma Dard-e-dil dard-e-jigar. A shekarar 1970 ne ya yi aikin Hajj tare da matarsa
Bilkis Rafi da kuma dan uwansa Muhammad Din. Ya rasu a shekarar 1980.
.
Sana Khan Jaruma ce da ta fi fitowa a fina-finan kudancin
indiya. Amma ta fito a wasu fina-finan na Mumbai
kamar fim din Toilet ek tha da Jai ho. A shekarar 2017 ne ta je aikin Hajj.
.
Source @bbchausa
COMMENTS