Blog Archive

Powered by Blogger.

Ba Zan Zalunce Ku ba Kuma bazan Bari A Zalunce Ku Ba- inji shugaba Buhari

Shugaba Muhammad Buhari ya bayyana cewa, zai ci gaba da yin iya bakin kokarinsa domin hana kansa da duk wani mutum zaluntar talakawan wannan...



Shugaba Muhammad Buhari ya bayyana cewa, zai
ci gaba da yin iya bakin kokarinsa domin hana
kansa da duk wani mutum zaluntar talakawan
wannan kasa. Buhari ya yi wannan furuci ne a jiya bayan
kaddamar da kudin akwati kimanin naira milyan
176.350 wadda aka gabatar jiya a filin taro na
Malam Aminu Kano dake birnin Dutse. Ya ce, kamar yadda gwamnatin APC ta kuduri
aniyar tabbatar da adalci, gaskiya da rikon
amanar al’ummar wannan kasa to babu ko
shakka zan iya bakin kokarina wajen kare
hakkinku a duk matakin da zan iya. ‘’Inaso in tabbatar muku cewa, da yardar Allah,
ba zan zalunceku ba, ba kuma zan bari wani
mutum ya zalunce ku ba, zan yi iya bakin
kokarina wajen kare hakkinku gamida tabbadar
da adalchi a tsakaninmu baki daya’’ inji shugaba
Buhari. Haka shugaba Buhari ya yabawa al’ummar
wannan kasa bisa fuskanta da suke nunawa
wannan gwamnati duk da irin halin kuncin da a
cewarsa tsohuwar gwamnata ta jefa al’umma a
ciki. Sannan ya kuma gamsu da yadda al’ummar
wannan kasa musamman ‘yan jihar ta Jigawa
suka karbi noma hannu biyu gami da habaka shi
wadda a cewarsa wannan zai taimaka matuka
gaya wajen farfado da tattalin arzikin wannan
kasa tamu baki daya. Shi kuwa da yake nasa jawabin a lokacin taron,
gwamnan jihar Jigawa Alhaji Muhammad
Abubakar Badaru ya ce wadannan kudade za’a
dunga turasu kowacce akwatu a kowanne wata
wadanda yawansu ya kai naira dubu 50 zuwa
100 domin gudanar da kananan ayyuka. Gwamnan ya ce, yin hakan zai taimaka matuka
gaya wajen magance kananan matsaloli kamar
gyaran rijiyoyin bada ruwan sha, masallatai,
motocin lafiya da dai sauransu. Haka kuma gwamnan ya yabawa
shugaba Buhari bisa ceto wannan kasa da yayi
daka tabarbarewar tattallin arziki gamida dorata
kan tirba ta gaskiya mai dorar da ci gaba. Daga karshe ya yaba wa dubban al’ummar da
suka tarbi shugaba Buhari gamida rokonsu bisa
bashi dama a karo na biyu domin dorewar ci
gaba da bunkasar tattalim arziki.
.
Source @bbchausa

COMMENTS

Name

Al'ajabi,13,Android zone,69,Applications,3,Aure,25,Blogger zone,1,computer zone,4,Dadin Kowa sabon salo,27,Facebook zone,12,Free Browsing,2,Hausa Films,1,Hausa novels,1,hotuna,2,Java zone,15,Kannywood,55,kiwon lafiya,35,Mata,12,Musics,24,Network,21,News,146,others,16,siyasa,81,Soyayya,3,Symbian zone,5,Video clips,33,video tutorials,3,Whatsapp,1,
ltr
item
Ameer: Ba Zan Zalunce Ku ba Kuma bazan Bari A Zalunce Ku Ba- inji shugaba Buhari
Ba Zan Zalunce Ku ba Kuma bazan Bari A Zalunce Ku Ba- inji shugaba Buhari
http://fm.nextwapblog.com/files/6475/buhari.jpg
Ameer
https://ameeryau.blogspot.com/2018/05/ba-zan-zalunce-ku-ba-kuma-bazan-bari.html
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/2018/05/ba-zan-zalunce-ku-ba-kuma-bazan-bari.html
true
2994989324915487916
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy