Majalisar dokokin kasar Uganda ta amince da wata sabuwar doka wadda za ta fara cajan 'yan kasar da ke amfani da shafin sada zumunta na W...

Majalisar dokokin kasar Uganda ta amince da
wata sabuwar doka wadda za ta fara cajan
'yan kasar da ke amfani da shafin sada
zumunta na WhatsApp harajin shlillings 200
(kimanin naira 20) a kullum. Har ila yau za su fara biyan harajin cinikayyan da
suka yi ta wayar salula, wato kashi 1 cikin 100 na
kudin da aka yi kowace cinikayya ta waya. Dokar za ta fara aiki ne a ranar 1 ga watan Yulin
bana. Sai dai wadansu 'yan majalisa uku sun nuna
adawarsu ga sabuwar dokar, inda suka bayyana
sabuwar dokar da "karabar haraji kashi-kashi,"
kamar yadda jaridar Daily Monitor ta ruwaito. 'Yan majalisa Robert Kyaggulanyi da Joshua
Anywarach da kuma Silas Aogon sun ce karin
haraji zai zama wani take 'yancin masu amfani da
WhatsApp saboda ana cajansu haraji kan katin
wayar da suke saya. Dan majalisar Arewacin Kasanda, Patrick Nsamba
na jam'iyyar adawa, ya ce: "Abu ne mai sauki dan majalisa ya ce harajin kaso 1
cikin 100 kudi ne kadan, amma ga mutanen da
suke samun kasa da dala a rana, kudi harajin kudi
ne mai yawa." A galibin kasashen duniya ba a biyan haraji kafin
amfani da kafar sada zumunta ta WhatsApp.
.
Source @bbchausa
COMMENTS