Ana zargin wani direban motar haya mai suna, Ayokunle, da kashe kansa a Anguwar Oke Ibukun, ta garin Ondo, da ke Jihar Ondo. A cewar wata ma...
Ana zargin wani direban motar haya mai suna,
Ayokunle, da kashe kansa a Anguwar Oke
Ibukun, ta garin Ondo, da ke Jihar Ondo. A cewar wata majiya, an sami Ayokunle, ne a
mace ranar Asabar a dakin sa, inda ake zargin ya
kashe kansa ne ta hanyar shan guba, bayan da
ya kasa biyan bashin da ya ci daga wata cibiyar
bayar da basuka. Majiyar ta ce, mamacin yana daga cikin
shugabannin kungiyar direbobi ta, ‘Road
Transport Employers Association of Nigeria,’ a
garin. Wani wakili a cikin kungiyar wanda bai soa
ambaci sunansa ba, ya ce, ya ga mamacin kwana
daya kafin mutuwar na shi, ya kara da cewa
kowa a Anguwar yana mamakin kashe kanshi
din da ya yi. Ya ce, “Mun yi mamakin jin ya mutuwar na shi a
ranar Asabar. Na gan shi ranar Juma’a, ba wani
alamun mutuwar sa a ranar Asabar, abin da
bakanta rai.” Da aka tuntube shi, Kakakin rundunar ‘yan sanda
na Jihar ta Ondo, Mista Femi Joseph, ya ce ba a
kawo masu rahoton aukuwar lamarin ba. “Na tuntubi dukkanin Ofisoshinmu na ‘yan sanda
da ke nan cikin garin na Ondo, duk sun ce ba a
kawo ma su rahoton aukuwar lamarin ba,” in ji
shi.
.
Source @hausaleadership
COMMENTS