'Yan Najeriya suna ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu game da kalaman da Shugaban kasar Muhammadu Buhari kan wutar lantarki a jawabinsa ...
'Yan Najeriya suna ci gaba da bayyana
ra'ayoyinsu game da kalaman da Shugaban
kasar Muhammadu Buhari kan wutar lantarki a
jawabinsa na ranar Dimokradiyya. Shugaban ya
ce an samu ci gaba ta fuskar samar da
hasken wutar lantarki yayin da yake yi wa 'yan kasar jawabi a ranar Talata, wato ranar da
gwamnatinsa ta cika shekara uku a kan mulki.
"'Yan Najeriya suna ba da labarin yadda wutar
lantarki ta inganta da kuma yadda suka rage
amfani da janareto," in ji shugaban. Har ila yau ya
ce a halin yanzu kasar tana samar da "MegaWatt 7,500"- an samu ci gaba daga
MegaWatt
5,222.3 wanda ta samar a watan Disambar 2017.
BBC ta samu dimbin ra'ayoyin jama'a a shafukan
sada zumunta bayan mun bukaci sanin ra'ayinsu
game da ikirarin shugaban a shafinmu na Facebook. Da gaske ne an samu ci gaba game da
wadata 'yan Najeriya da hasken wutar lantarki
kamar yadda Shugaba Buhari ya yi ikirari a
jawabinsa na ranar Dimokradiyya. bbchausa.com
Posted by BBC Hausa on Tuesday, 29 May 2018
Yayin da wasu 'yan kasar suka musanta ikirarin shugaban, wasu kuma sun gasgata ikirarin
shugaban. Asy Kano:"Toh ni dai gani a gidana
babu wutar lantarki tun safe, har zuwa yanzu
tara na dare..
Dama mun Saba sai 12 dare suke kawowa su
dauke 3 ko 4 na asubahi. Dole muke neman fetur domin mu tayar da inji saboda azumi ga kuma
yara
kanana basa iya barci saboda zafi ..mu dai kam
bamu ga wata ci gaba ba akan harkar wutar
lantarki a Najeriya." Amma Zubairu Bello gasgata
kalaman shugaban ya yi: "Kwarai kuwa, zancen Shugaba Buhari gaskiya ne. An samu ci gaba a
bangaren wutar lantarki. Kuma
ina fatan kamfanin wutar lantarki ya koma
karkashin ikon gwamnatin tarayya a maimakon
'yan kasuwa." Godiya Markus kuma cewa ya yi:
"A gaskiya mu har yau babu wani canji dangane da wutar lantarki.
Mu a Tafawa-Balewa da ke jihar Bauchi mun
manta
ranar da aka kawo wutar lantarki.Yanzu haka a
babban asibitin gwamnati na kwana, amma sai
yawan sauro. Kai ko dakin ajiye gawa janareta ake
amfani da shi." Amma Suleiman Issa ya ce a inda
yake suna samun wuta: "Wannan gaskiya ne
saboda a nan Lagos a inda
nake zama a Opebi a Ikeja. Yau fiye da mako
daya a wuni da wuta a dauke wuta sau daya, kafin ka ta
da janarato an kawo wutar saboda haka duk
wanda ya ce ba'a samu cigaba ba sai dai ko ta
wani
fannin daban. Ga sauran wadansu ra'ayoyin
jama'a - kuma za ku iya bayyana ra'ayoyinku a shafin namu na
Facebook:
.
Source @bbchausa
COMMENTS