Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewar, fiye da mayakan kungiyar Boko Haram 700 Boko Haram suka nuna aniyarsu na mika wuya, a dai dai lokacin d...

Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewar, fiye da
mayakan kungiyar Boko Haram 700 Boko Haram
suka nuna aniyarsu na mika wuya, a dai dai
lokacin da gwamnatin take kara bayyana irin
halin tashin hankalin da yakin da ahka shekara 9
ake gudanarwa ya shafi rayuwar mutanen dake zaune a yankin Arewa maso Gabas. Ambasadan Nijeriya kuma wakili na dindindin a
majalisar dinkin duniya, Tijjani Bande, ne ya
bayyana wa kwamitin tsaro na majalisar dinkin
duniya cewa, mutane fiye da Miliyan 14.8 ne
rikicin ya shafa. Ya ce, an tarwatsa mutane Miliyan
1.7, sun zama ‘yan gudun hijira, mafi yawan wadanda lamarin ya shafa kuma kananan yara
ne da mata. Mista Bande na jawabi ne a wahen wani
tattaunawa a kan hanyoyin kare fafaren hula a
yayin da ake gudanar da yaki da muggan
makamai. Ya tabbtar wa kasashen duniya da
cewa, shirin da gwamnatin Buhari ked a shi mai
suna ‘The Buhari Plan’ zai kawo sauki matuka a yankin Arewa maso gabas inda ‘yan kungiyar
Boko Haram ke cin karensu babu babbaka duk
kuwa da matakai na soji da ake kai musu. Kwamitin shugaban kasa a kan Arewa maso
gabas ce ta, samar da tsarin ‘The Buhari Plan’ –
tsari ne da aka shirya zai sake tsugunar da
wadanda ta’addanci ya cutar a cikin shekaru 9 da
aka yin a ci gaba da yakin da kuma farfado da
garuruwan da yakin ya tarwatsa. Mista Bande ya kara da cewa, an samar da tsarin
“Social Protection Initiatibe” da “National Action
Plan” domin aiwatar da cikakken tanaden
tanaden da dokan majalisar dinkin duniya mai
lamba 1325 (2000), an fitar da shi ne saboda
kare fararen hula musamman mata da kananan yara daga cutarwar da dakarun Boko Haram
suka yi wa jama’a. “A kan haka, wadannan shirye shiryen zasu
taimaka wa aiwatar da tsarin nan na ‘The Buhari
Plan’, wanda ya fitar da tsari dalla dalla yadda za a
samar da agaji da farfado da tattalin arzikin
yankin Arewa maso Gabas da kuma sake
tsugunar da wadanda suka tarwatse daga gidajen su. “A halin yanzu muna hadin kai da kasshe
makwabtanmu kamarsu Chad da Cameroon da
Niger da kuma Benin, ta hadakar jami’an tsaro na
“Multinational Joint Task Force” domin karya
alkadarin kungiyar Boko Haram, wadanda ke
harin mata da yara kanana”. Tsarin “Buhari Plan” nada nufin cimma
tsaftataccen yankin Arewa maso gabas da zai
zama abin alfahari ga duniya baki daya a fannin
farfadowa bayan fuskantar rikicin ‘yan ta’adda. Ambasadan ya kuma kara da cewa, Nijeriya na
daya daga cikin kasashen da suka rungumi tsarin
nan na “Safe Schools Declaration” da aka
kaddamar a garin Oslo, inda akayi alkawarin kare
makarantu a yayin da ake fuskantar yaki tare
kuma da kare manyan makarantu da jami’o’i daga fadawa amfanin ‘yan kungiyar Boko Haram
a yayin yaki da makamai. Miata Bande, ya kuma ce, wannan sanarwa ta
kara karfafa Nijeriya a tsarin nan nata na
“Nigeria’s national Safe Schools Initiatibe” da aka
kafa a shekarar 2014, a matsayin martanin
gwamnatin tarayya wajen samar da amintaccen
yanayin gudanar da karatu. Ya ce, wannan shirin, yana nuna kudurin
gwamnatin tarayya na tabbatar da tsaro ga mata
da kananan yara a lokacin da ake yaki da
makamai, domin samar dasu a yayi da ake yaki,
ta yadda za a samu kare aukuwar yakin da sake
gina garuruwar da yakin ya lallata. Ambasadan ya kuma ce, “Ya kamata jama’a su
sani cewa, an yi garkuwa da mata da kananan
yara da yawan gaske, amma tuni aka kubutar
dasu , sannan dukkan wuraren da ‘yan ta’adda
suka mamaye an karbosu. “abin da muke gani a yakin tabkin Chadi ya zama
hujjar cewar, in har akwai karfin hali da taimakon
kasashen waje za a iya murkushe ta’addanci. “Haka kuma gwmnatin Nijeriya ta samar da wani
shiri na musamman mai suna ‘Operation Safe
Corridor’, domin tabatar da sake tsugunar da
kuma sake mayar da ‘yan ta’adda cikin al’umma,
musamman wadanda suka nemi mika wuya da
radin kansu daga cikin mayakan Boko Haram zuwa ciki al’umma.”. Ambasadan na Nijeriya ya kara da cewa, da yawa
daga cikin ‘yan ta’addan sun mika wuya ga
hukumomin sojoji da radin kansu yayin da fiye
da 700 suka nuna aniyarsu na mika wuya. Ya ce, gwamnatin Nijeriya ta dauki matakin kula
da wadanda ‘yan Boko Haram suka cutar
musamman ta hanyar fyade da cin zarafi da
sauran laifukkan yaki. Ya kuma bayyana cewa, wadanan matakan sun
hada da samar da kayayyakin agajin gagawa da
kudaden jari, ga masu sana’a da kumam bayar da
tallafin karatu ga matasan yankin Arewa maso
gabas. “duk da kokarin da ake gudanarwa a matakin
kasa, muna da cikakken sanin cewa, kare fararen
hula a yayin yaki da makamai abu ne mai
matukar mahimmanci, ba wai ga majalisar dinki
duniya kadai har ma das aura kasashen duniya
gaba daya. “A saboda haka muna matukar bukatar agajin
gamayyar kasashen duniya domin maganin
matsalar. “A kan haka muna mika jinjina ga sojojinmu da
sauran masu ruwa da tsaki da sauran kungiyoyi
a bisa kokarinsu na aiki tukuru domin tabbatar
da tsaron fararen hula a yayin yakin da ake
gudanarwa” inji Mista Bande.
.
Source @bbchausa
COMMENTS