Blog Archive

Powered by Blogger.

[Android] Yadda ake chanja version na wayar Android zuwa kowane irin version darasi na (5) na Karshe Yanda ake Dora Custome Rom

Idan mai karatu bai mantaba a darasinmu na baya wato darasi na Hudu (4) mun tsaya akan yanda zakuyi backup na stock custome Rom din wayarku ...


Idan mai karatu bai mantaba a darasinmu na baya wato darasi na Hudu (4) mun tsaya akan yanda zakuyi backup na stock custome Rom din wayarku to yau insha Allah zamu dora darasi na biyar(5) kuma shine darasi na karshe, wato wannnan darashin shine na yanda zaka dora kowane irin file/verion akan wayar taka ta android, tunda abaya munyi bayanin yanda zaku ajiye ainihin file/rom din wayar taku akan memory da kuma yanda zaku dawo dashi ainihin kan wayar
.
Yauwa kamar de yanda abaya nayi bayanin yanda zaku sanya Recovery img da kuma yanda ake shiga Recovery akowace irin waya, sannan nayi bayanin yanda zaku ajiye Rom/file dinku akan memory da kuma yanda zaku dawo dashi, idan baku mantaba duk wannan abubuwan daya zayyano nace anayinsune ta hanyar shiga Recovery ina fatan mai karatu yana biye damu,
.
Yauwa to yanzu abun da zakuyi shine, kuje google kuyi download na Rom din da kukeso ku dora a wayar taku misali kuna da android version 4.4 kitkat, kamar su Y2 Y3 da sauransu to kukuma kunaso ku mayar da ita version 5.0 lollipop kamar su gionee p5 ko tecno c8, to idan zakuyi download na Rom din saiku Rubuta a google kamar haka,
.
Misali kana da waya Tecno Y2 kanaso ka mayar da ita version 6 marshmallow, to saika Rubuta kamar haka Download tecno y2 6.0 custom rom, duk rom din wayar da zaka dauko haka zakayi da zarar kayi haka insha Allah zasu baka shi, sai kayi download dinsa ammafa, suna da nawi dan haka saika dan nemi Data/mb mai dan yawa,
.
Bayan kunyi download dinsa saiku ajiyeshi akan memory dinku, akan memory fa kada ku dorashi akowane folder kawai akan memory, da zarar kun gama dorashi akan memory, shikkenan yanzu saiku sanya wayar taku a Recovery domin sanya wayar saiku saika kashe wayar taka. Sannan yanzu saika kunna idan ka tashi kunna wayar saika danne Madannin kunna wayar tare
da wajen Kara Volume na wayar duk ka dannesu a lokaci daya, wato wajen kunna waya da wajen kara volume su zaka danne. Da zarar ka danne bayan wadansu seconds zata kawo sannan zata kawoka cikin Recovery dinnan daka dora to karka damu yayin data kawo zakaga ta nuno Rubutu kamar haka:
.
--reboot system now


--Install Zip From SDcard


--Wipe data/factory Reset


--Wipe cache Partition


--backup and restore


--Mounts & Storage


--Advance
.
Wannan Rubutun da ta jero sune Recovery din daka dora to yanzu abin da zakayi saika shiga Inda aka Rubuta: Install Zip From SDcard idan ya bude saika Shiga inda aka Rubuta Choose zip From Sdcard da zarar ya bude zakaga ta jeroma foldodi na Memory dinka, to karka damu ka duba Zakaga wannan Rom din da kayi download wanda nace ka ajiyeshi akan memory, to da zarar ka ganshi sai kaje kansa ta hanyar danna madannin Rage volume, da zarar kahau kansa, saika danna wajen kunna wayar da zarar ka danna nan Ta ke zakaga ta fara dora maka wannan Rom din, to saika jira har saita gama, amma tana dan daukan Lokaci dan haka karka damu, kawai ka jira ta gama, idan ta gama zata nunama Install Complate shikkenan file ya doro, yanzu saika duba inda aka Rubuta reboot system now saika Shiga daka shiga zakaga wayar ta kunnu, shikkenan tana kunnuwa zakaga sauyi, domin kuwa nan take zakaga komi na wayar ya chanja, tun daga kan Boot animation har boot sound, duk tsarin wayar taka zai koma na sabon Rom din daka, dora misali idan wayar taka Version 4 ce kitkat, to da zarar ka gama install na rom dinnan nan take, zakaga ta koma rom din daka dora idan rom din marshmallow ka dora to zakaga wayar ta juya zuwa mashwollow, kuma kaima daga yanzu insha Allah duk abin da mai version 6 zaiyi kaima zakayi.
.
Ina fatan kun gane wannan darasin
.
Yanzu ga yanda zaku dawo da ainihin rom dinku, wato yanda zaku dawo da wayarku zuwa ainihinta misali wayarku version 4 ce sai kuka mayar da ita version 5 ko 6, kuma sai kuka gaji da version din kode wani abun dabam to ga yanda zaku dawo da Rom din, naku.
.
Idan baku mantaba a darasinmu na baya, wato darasi na 4 munyi bayanin yanda zakuyi Backup na
stock/custome Rom na wayarku ta android wato yanda zaku ajeye ainishin rom din wayar taku,
To wannan Rom din da mukayi bayin yanda ake ajiyeshi to shine ainihin wayar taku yayin da kuka chanja wani rom din kuma daga baya kukeso ku dawo da ainihin naku, to shide wanda mukayi bayanin abaya to shine wanda zaku dawo din dashi dan haka ga yanda zakuyi ku dawo dashi
.
Da farko ku sanya wayar taku a Recovry mun riga mun fadi yanda ake sanya waya a recovery wato akashe waya idan an tashi kunnawa sai a danne madannin kara volume da kuma wajen kunna wayar duk a lokaci daya da zarar an danne zata kawoku nan wato zata jero irin wannan rubutun na kasa to saiku shiga
--reboot system now


--Install Zip From SDcard


--Wipe data/factory Reset


--Wipe cache Partition


--backup and restore


--Mounts & Storage


--Advance
.
Saiku shiga --backup and restore da zarar kun shiga zakuga inda aka
Rubuta ==> Restore <== saiku shiga da zarar kun
shiga zai farayi muku Restoring na ainihin Rom
din naku bayan wadansu mintuna zai gama da
zarar ya gama zai nunama Finish shikkenan ka
gama saika dawo ka shiga Reboot system shikkenan ka gama zakaga tsarin ka ya dawo yanda yake, ina fatan kun gane.
.
Wannan cikykykyan bayanin yanda ake chanja version na wayar Android, da fatan duk wanda ya karanta wannan darasin ya fashinta, Allah ya bada sa,a
.
Domin karin bayani ko tambaya
call: 08169872309
.
.
.
Kada ku manta ku tura wannan darasin zuwa abokanku,
.
Mungode

COMMENTS

Name

Al'ajabi,13,Android zone,69,Applications,3,Aure,25,Blogger zone,1,computer zone,4,Dadin Kowa sabon salo,27,Facebook zone,12,Free Browsing,2,Hausa Films,1,Hausa novels,1,hotuna,2,Java zone,15,Kannywood,55,kiwon lafiya,35,Mata,12,Musics,24,Network,21,News,146,others,16,siyasa,81,Soyayya,3,Symbian zone,5,Video clips,33,video tutorials,3,Whatsapp,1,
ltr
item
Ameer: [Android] Yadda ake chanja version na wayar Android zuwa kowane irin version darasi na (5) na Karshe Yanda ake Dora Custome Rom
[Android] Yadda ake chanja version na wayar Android zuwa kowane irin version darasi na (5) na Karshe Yanda ake Dora Custome Rom
https://img.gadgethacks.com/img/82/38/63504226410381/0/flash-custom-rom-onto-your-samsung-galaxy-note-2-and-enhance-your-android-experience.w1456.jpg
Ameer
https://ameeryau.blogspot.com/2018/05/android-yadda-ake-chanja-version-na.html
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/2018/05/android-yadda-ake-chanja-version-na.html
true
2994989324915487916
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy