Tsohon gwamnan Kano kuma jigo a jam'iyyar adawa ta PDP ya ce gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari bata tabuka wani abun azo a gani ba a ts...
Tsohon gwamnan Kano kuma jigo a jam'iyyar adawa ta PDP ya ce gwamnatin Shugaba
Muhammadu Buhari bata tabuka wani abun azo
a gani ba a tsawon fiye da shekara uku da ta yi
kan mulkin kasar. Malam Ibrahim Shekarau, wanda ke neman
jam'iyyar ta tsayar da shi takarar shugaban kasa a
zaben 2019, ya shaida wa BBC cewa gwamnatin
Buhari na tafiyar da mulki "tamkar ba ta san abin
da take yi ba". "Hatta wadanda suke adawa da gwamnatin sun yi
mamakin yadda ta gaza wurin aiwatar da
abubuwan da ta yi alkawari," in ji Shekarau, wanda
a baya ya yi tafiyar siyasa tare da Shugaba Buhari. Ya kara da bayyana rawar da gwamnatin ta taka da
cewa ba yabo ba fallasa. Sai dai ana ta bangaren, gwamnatin APC tana bugar
kirjin cewa ta farfado da tattalin arzikin kasar,
wanda jam'iyyar PDP ta "ruguza" a shekara 16 da
ta shafe tana mulki. Sannan ta ce ta sanya kasar a kan turbar dogaro da
hanyoyin samun kudaden shiga daban da man
fetur.
A 'yan kwanakin baya ne Shugaba Muhammadu
Buhari ya bayyana aniyarsa ta neman wa'adi na
biyu a zabe mai zuwa. Sai dai wasu masana na ganin zai fuskanci zazzafan
kalubale ganin yadda wasu jama'a da dama suka
dawo daga rakiyar yadda ya ke gudanar da
gwamnatinsa. Tsohon gwamnan jihar ta Kano ya ce zai sauya
fasalin yadda ake gudanar da mulki idan ya zama
shugaban kasar. Ya kuma musanta zarge-zargen cewa yana da
hannu a rarraba kudaden da ake zargin an
wawure gabannin zaben 2015. Har yanzu dai rahotanni sun nuna cewa Hukumar
Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC na bincike
kan lamarin, amma ba su kai lamarin gaban kotu
ba.
.
Source @bbchausa
COMMENTS