Iyayen wani matashi dan shekara 30 sun kai shi kara kotu saboda ya ki bar musu gida, bayan da ya kai munzalin yin hakan a ganin su. Takardun...
Iyayen wani matashi dan shekara 30 sun kai
shi kara kotu saboda ya ki bar musu gida,
bayan da ya kai munzalin yin hakan a ganin su. Takardun kotu sun nuna cewa matashin mai suna
Micheal Rotondo, ba ya biyan kudin haya, kuma ba
ya taya iyayensa da ayyukan gida, sannan ya ki
karbar kudin da iyayensa suka ba shi don ya je ya
fara tasa rayuwar. Bayan wasiku biyar da aka ba shi na kora, Christina
da Mark Rotondo sun ce har yanzu dan nasu ya ki
barin gida. Michael yana musun cewa a bisa doka, ba a ba shi
cikakken wa'adin barin gidan ba. Mista da Misis Rotondo sun kai kara a ne kotun
kolin yankin Onondaga, kusa da Syracuse, a New
York, a ranar 7 ga watan Mayu, bayan sun shafe
watanni suna kokarin ganin dan nasu ya bar
gidan. Lauyan Micheal, Anthony Adorante, ya shaida wa
kafar watsa labarai ta Syracuse.com, cewa
ma'auratan ba su san wata hanyar da za su bi don
sallamar dan nasu daga gidan ba. Wasikar ta farko da aka karanta ranar 2 ga watan
Fabrairu a kotun ta bayyana cewa: "Mun yanke
shawara cewa sai ka bar gidan nan ba tare da bata
lokaci ba." Yayin da Micheal ya yi watsi da wasikar, sai
iyayensa suka sake rubuta wasikar kora ta
musamman tare da agajin lauyansu. A wasika ta biyun da aka rubuta ranar 13 ga watan
Fabrairu ta ce: "Don haka muka yanke shawarar
korarka daga gidan nan." "Za mu dauki matakin shari'a idan ba ka bar gidan
nan ba zuwa ranar 15 ga watan Maris din 2018," a
cewar wasikar. Daga baya iyayen nasa sun ce za su ba shi dala
1,100 (kusan naira 400,000) ya bar gidan - tare da
yayyaba masa bakar magana. "Akwai ayyuka da irin ku da ba su taba sanin
yadda ake aiki ba ma za su iya samu. Ka je ka nema
- dole ka nemi na kanka!," in ji iyayen. Amma a ranar 30 ga watan Maris, sai ta bayyana
karara yaron ba shi da niyyar barin gidan. A watan Afrilu ne Mista da Misis Rotondo suka je
kotun kauyensu don ganin kotu ta kore shi daga
gidan. Sai aka gaya musu cewa sai sun samu izini daga
Kotun Koli, ita za ta sa shi dole ya bar gidan tun da
Micheal dansu ne. Kamar yadda kafar watsa labaran WABC ta shaida,
Micheal ya bayyana karar da iyayensa suka kai a
matsayin ramuwar gayya kuma ya bukaci kotun ta
yi watsi da ita. Zuwa karshen watan nan, kotun kolin za ta yanke
hukunci kan karar - makonni kadan kafin Micheal
ya cika shekara 31.
.
Source @bbchausa
COMMENTS