Blog Archive

Powered by Blogger.

Turawa sun bukaci da a gaggauta cire ayoyin dake sukar Yahudu da Nasara daga Al-Qurani

Jiga-jigan gwamnatin Turkiyya na ci gaba da tofin Allah tsine kan da'awar da tsohon shugaban Faransa,NicolasSarkozy da wasu gungun mutan...



Jiga-jigan gwamnatin Turkiyya na ci gaba da tofin
Allah tsine kan da'awar da tsohon shugaban
Faransa,NicolasSarkozy da wasu gungun mutane
300 suke yi na a gaggauta cire duk wasu ayoyin da ke sukar Yahudawa da Kiristoci daga Al Kur'ani mai
tsarki.
A jerin mutanen da ke sahun gaba wajen yin
wannan farfagandar akwai,
Tsohon shugaban kasar Faransa,NicolasSarkozy,
Philippe Val, tsohon shugaban jaridar "Charlie Hebdo" wacce daman ta yi kaurin suna wajen yin
zanen batanci kan mafificin halitta,Manzon Allah
Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare
shi,
Sai tsohon magajin garin birnin Paris,Bertrand
Delanoe, Sai tsoffin ministoci 3,
Sai jiga-jigan addinai daban-daban,
masana,taurarunfina-finai,masuaikin hannu da dai
sauran su.
Masu wannan bakar da'awar suka ce,"
A gaggauta share duk wasu ayoyin da ke kiran Musulmai da su kyamaci ko kuma su yaki
Yahudawa da Kiristoci.
Saboda barin su, babbar barazana ce ga rayuwar
mabiya wadannan addinan".
Kamar a sauran sassan duniya, samun wannan
labarin ke da wuya,shugabannin kasar Turkiyya suka yi tofin Allah tsine da kuma tsawatarwa
Farasansawan.
A shafinsa na Twitter,mai magana da yawun
shugaban kasar Turkiyya,Ibrahim Kalin ya ce,"
Al Kur'ani,littafine mai tsarki.
Allah zai ci gaba da tsare shi har karshen duniya. Al Kur'ani ba allo ba ne da za a dinka rubutu
kansa,kana a dinka goge shi a duk lokacin da aka
ga dama.
Littafinmu ne mai tsarki.Kyamar Yahudawa akida ce
da ta bulla a tsakiyar Turai.
Turawan da ke bukatar warware bakin zaren wannan matsalar, su waiwayi baya don bincikar
tarihinsu.
Babu wani jahilci da ya kai wannan bukatar tasu,a
wannan duniyar tamu ta yau,inda ake tinkaho da
wayewa".
Mataimakin shugaban gwamnatin Turkiyya,Bekir BozdaÄŸ ma ya wallafa albarkacin bakinsa a Twitter
inda ya ce,"Daya daga cikin manya-manyan
makiyan Islama,tsohon shugaban Faransa da wasu
gungun Faransawa 300 sun shafa wa Islama bakin
fenti ta hanyar bayyana bukatarsu ta a gaggauta
cire "Ayoyin da ke kiran jama'a da su kyamaci Yahudawa da Kiristoci" daga Kur'ani.
Wadannan su ne shashashu, sakarkaru,marasa
tunani, gidadawa,danginAbu Jahil, kana 'yan
DAESH a Yamma.
Ba Sarkozy ba,ko da illahirin makiya Islama za su
hade mana kai,ba zasu taba kawo daidai da aya daya tilo ko kuma sauya wani abu daga cikin
Kur'ani, har sai an busa kaho".
Ministan harkokin wajen Turkiyya, Mevlüt
Çavuşoğlu kuma cewa ya yi,"
Wannan wata alama ce da ke nuna irin yadda
kyama da nuna wariya ga Musulmai suka kamari a Turai.
Tuni wadannan mutane suka wuce gona da iri.
Shin me kuke tsammanin zai afku, bayan da suka
furta irin wadannan kalaman ?
Za a dinka kai wa masallatai hare-hare a Turai.
A tsawon tarihinku kun ci gaba da zaluntar Yahudawa.
Musulmai ne suka cece su ta hanyar karbar
bakwancinsu hannaye biyu a tsawon karnoni da
dama, musamman ma a zamanin daular Musulunci
ta Usmaniyya,inda aka kare martabarsu tare da
karrama su. Bamu san me ake nufi da kyamar Yahudu ba.
Don babu irin wannan akidar a addini da kuma
littafinmu.
Yayin da a yau, a Turai ,nuna wariyar launin
fata,kyamar masu neman mafaka da 'yan gudun
hijira da kuma waninsa, ke ci gaba da samun gindin zama.
Jam'iyyun siyasa masu wariyar launin fata na cin
karansu babu babbaka a kasashenku.
In dai da gaske kuke,ku fara yakar su mana?.
Shin wannene 'yancin da kuke ambato?
Shin wa zaku bai wa darasi?". Ministan yawon bude ido da raya al'adu na
Turkiyya,Numan KurtulmuÅŸ ma, ya nuna bacin
ransa inda ya ce,
"Wannan batun da suka zo da shi ba komai ba ne
face, gidadanci da kuma wauta.
Allah wadai ga wadanda ke sukar mabiya wannan tsarkaken littafin "Kur'ani" da kuma wannan
babban addinin mai suna salama "Islam".
Ina fatan al'umar kasashen Turai zasu yi kunnen
uwar shegu da wadannan maganganun na badala
da rashin hankali"
.
Source @rariya

COMMENTS

Name

Al'ajabi,13,Android zone,69,Applications,3,Aure,25,Blogger zone,1,computer zone,4,Dadin Kowa sabon salo,27,Facebook zone,12,Free Browsing,2,Hausa Films,1,Hausa novels,1,hotuna,2,Java zone,15,Kannywood,55,kiwon lafiya,35,Mata,12,Musics,24,Network,21,News,146,others,16,siyasa,81,Soyayya,3,Symbian zone,5,Video clips,33,video tutorials,3,Whatsapp,1,
ltr
item
Ameer: Turawa sun bukaci da a gaggauta cire ayoyin dake sukar Yahudu da Nasara daga Al-Qurani
Turawa sun bukaci da a gaggauta cire ayoyin dake sukar Yahudu da Nasara daga Al-Qurani
http://fm.nextwapblog.com/files/6475/qur-an.jpg
Ameer
https://ameeryau.blogspot.com/2018/05/turawa-sun-bukaci-da-gaggauta-cire.html
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/2018/05/turawa-sun-bukaci-da-gaggauta-cire.html
true
2994989324915487916
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy