Al'ummar Musulmi a Ghana sun yi watsi da shawarar da aka bayar na cewa limamai su rinka kiran sallah ta manhajar Whatsapp, inda suka ce ...

Al'ummar Musulmi a Ghana sun yi watsi da
shawarar da aka bayar na cewa limamai su
rinka kiran sallah ta manhajar Whatsapp, inda
suka ce abu ne da ba za su "taba yarda ba." Hakan dai ya biyo bayan kiran da ministan muhalli,
kimiyya da fasaha, Farfesa Frimpong Boateng, ya yi
cewa ya kamata limamai su ajiye amfani da lasifika
wajen kiran sallah, su koma amfani da tura sakon
waya ko kiran ta manhajar WhatsApp. A cewar Ministan, hakan zai rage hayaniya a kasar. What do you know about the call for people to prayer?? If you can't say something relevant then shut up! Posted by Abdulai Issahaku Muślim on Tuesday, 10 April 2018 Farfesa Boateng ya ce, 'Me ya sa idan lokacin sallah
ya yi ba za a iya sanar da mutane ta sakon wayar
salula ko WhatsApp cewa lokacin sallah ya yi ba? "Ai sai limami kawai ya aika da sako ta WhatsApp
ya sanar da mutane cewa kowa ya hallara a
masallaci za a yi sallah". To amma mai magana da yawun babban limamin
kasar, a wata tattaunawa da yayi da sashen
Turancin Broka na BBC ya yi watsi da kiran, inda ya
ce 'Kiran sallah da murya a musulunci al'adace da
aka saba wadda aka gada tun kaka da kakanni,
kuma wannan abune da ba za mu canja shi ba'. Wani Musulmi ne a shafin sada zumunta, ya yi suka
a kan abin da ministan ya ce, inda ya ce sam bai
dace ba.
.
Source @bbchausa
COMMENTS