A ranar Larabar , 2 ga Mayu, 2018, fitacciyar jarumar finafinan Hausan nan, Hajiya Hauwa Maina, ta riga mu gidan gaskiya. Ta rasu ne ta na d...
A ranar Larabar , 2 ga Mayu, 2018, fitacciyar
jarumar finafinan Hausan nan, Hajiya Hauwa
Maina, ta riga mu gidan gaskiya. Ta rasu ne ta na
da shekaru 48 da haihuwa a asibitin Malam
Aminu Kano da ke birnin Kano bayan ta sha jinya. Majiyarmu ta shaida wa wakilinmu cewa,
marigayiyar ta fara kwanciya ne a Federal Staff
Hospital da ke Abuja, inda daga bisani a ka mayar
da ita can Kano din. Majiyar ta cigaba da cewa, gabanin kwanciyar
Marigayiya Hauwa jinyar, ta yi fama da lalurar a
tsai-tsaye ne, inda a ka lura da cewa, ta rame
sosai. Daya daga cikin masu ruwa da tsaki na
Kannywood da ke Kaduna kuma jarumi, sannan
daraktan finafinai, Malam Al-Amin Ciroma, ya
shaida wa wakilinmu cewa, marigayiyar ta rasu
ne da misalin karfe tara na daren Larabar kuma
za a yi jana’izarta da safiyar Alhamis din nan. Tuni dai abokan sana’arta su ka shiga aika wa da
sakonnin ta’aziyya ga juna a kafafen daban-
daban, musamman ma zauren nan na masu ruwa
da tsaki a masana’antar shirin fim din Hausa, wato
Kanyywood Vanguard da kuma sauran kafafen
sadarwa na zamani. Hauwa Maina ta rasu ta bar ’ya’ya biyu, mace da
namiji.
.
Source: @leadershipayau
COMMENTS