Shugaban ya bayyana hakan ne a wani bangare na jawabinsa na bikin Ranar Dimokuradiya da ya gabatar a ranar Talata da safe. Ya ce: "Nan ...
Shugaban ya bayyana hakan ne a wani bangare na
jawabinsa na bikin Ranar Dimokuradiya da ya
gabatar a ranar Talata da safe. Ya ce: "Nan da 'yan kwanaki kadan zan sadu da
matasa da dama na kasar nan domin sanya hannu
kan kudurin dokar da za ta bai wa matasa damar
tsayawa takara." A watan Yulin 2017 ne Majalisar dattawan kasar ta
amince da kudirin da zai bai wa matasa damar
tsayawa takarar a mukaman shugaban kasa da
gwamna da majalisun dattawa da na wakilai. Kudirin dai ya bai wa matasa masu shekara 35
damar shiga takarar neman shugabancin kasar
yayin da ya bai wa matasa masu shekara 30 damar
neman gwamna. Haka zalika, kudurin ya amince 'yan shekara 25 su
tsaya takarar zama wakilai a majalisar wakilan
kasar. Ana ganin wannan matsaya ta shugaban kasa a
wani gagarumin ci-gaba, kuma wasu matasan
kasar sun nuna farin cikinsu kan wannan lamari. A baya dai mutane da dama sun nuna shakku kan
ko shugaban zai amince ya sa hannu kan dokar. Sauran sakon shugaban kasa A cikin jawabin nasa, Shugaba Buhari ya tabo
batutuwa da dama na irin sauye-sauyen da
gwamnatinsa ta kawo cikin shekara uku, da kuma
wadanda take burin kawowa nan gaba. Ya yi magana kan yadda cikin shekara uku aka
samu 'gagarumar nasara' wajen dakile ayyukan
masu tayar da kayar baya na Boko Haram, da ceto
da yawa daga 'yan matan Chibok da 'yan matan
Dapchi da wasu mutum 16,000 da 'yan kungiyar
suka sace, da kuma tabbatar da tsaro a sansanonin 'yan gudun hijra. Sai dai wasu masu sharhi sun sha fadar cewa har
yanzu da sauran rina a kaba dangane da batun
magance rikicin Boko Haram, ganin yadda 'yan
kungiyar ke ci gaba da kai hare-haren kunar bakin
wake. Rikicin manoma da makiyaya Shugaba Buhari ya tabo batun yadda ake samun
karuwar rikice-rikice tsakanin manoma da
makiyaya a jihohin kasar da dama, yana mai cewa
al'amarin ba mai dadi ba ne, amma "gwamnati na
iya bakin kokarinta don ganin an magance
wannan matsala."Ya kuma tabo batun yadda gwamnatinsa ta samu
nasara a yaki da cin hanci da rashawa, da samar da
ayyukan yi da kuma bunkasa tattalin arziki. Shugaba Buhari, wanda ya dare mulkin kasar a
2015, ya ayyana aniyarsa ta sake tsayawa takara a
2019. Sai dai ana yawan sukarsa kan yadda gwamnatinsa
ta kasa ciyar da tattalin arzikin kasar gaba, amma a
jawabin nasa na ranar Talata, ya ce duk da irin
kalubalen da ake fuskanta, a yanzu tattalin arzikin
na bunkasa.
.
Source @bbchausa
COMMENTS