Rahotanni daga jihar Legas da ke kudu maso yammacin Najeriya, na cewa wata mata ta kashe mijinta bayan ta yanke ma sa mazakuta. 'Yan san...
Rahotanni daga jihar Legas da ke kudu maso
yammacin Najeriya, na cewa wata mata ta
kashe mijinta bayan ta yanke ma sa mazakuta. 'Yan sanda a jihar sun ce, matar ta kuma yi
yunkurin kashe kanta amma makwabtanta suka
shiga suka hana ta. An dai yi amannar cewa, ma'auratan lauyoyi. Kawo yanzu matar ada ake zargi ba ta ce komai ba
kan wannan batu. 'Yan sandan jihar sun ce, an kira su ne daga wani
rukunin gidaje mai suna Diamond Estate da ke Ajah
a yankin Lago a jihar ta Lagos da safiyar ranar
Alhamis inda aka ba su labarin cewa wata mata ta
kashe mijinta a rukunin gidajen. Nan da nan ba a yi wata-wata ba, sai aka tura wasu
'yan sanda wajen, inda da zuwansu suka tarar da
mutumin a kwance cikin jini a kan gado. Masu bincike sun ce, wadda ake zargi da aikata
kisan ita ce matarsa, kuma ta yi amfani da wuka ne
ta cakawa mazakutarsa a wurare daban-daban. Kazalika ita ma ta yi yunkurin kashe kanta, kafin
mutane suka hana ta. Yanzu haka matar na asibiti tana karbar magani. Mai magana da yawun 'yan sanda a jihar ta Legas,
Chike Oti, ya ce ma'auratan sun yi aure ne shekaru
da suka wuce, to amma auren na cike da tashin
hankali. Ya ce tun lokacin da aka yi auren ba a zaman lafiya. Irin wannan ya taba faruwa a Abuja, babban birnin
tarayyar Najeriya, inda ake zargin wata mata da
kashe mijinta ta hanyar da ba masa wuka. Lamarin dai ya faru ne a watan Nuwambar 2017,
inda aka gabatar da ita a gaban kotu, kuma har
yanzu ana shari'ar, ba akai ga yanke ma ta hukunci
ba. Sai dai matar mai suna Maryam Sanda, ta musanta
zargin da ake yi mata.
.
Source: @bbchausa
COMMENTS