Tsohon Jakadan Amurka a Najeriya, John Campbell, ya ce idan har Najeriya ta ci gaba da tsare shugaban kungiyar 'Yan Uwa Musulmi ta Shi...
Tsohon Jakadan Amurka a Najeriya, John Campbell, ya ce idan har Najeriya ta ci gaba da
tsare shugaban kungiyar 'Yan Uwa Musulmi ta
Shi'a (IMN) to za a iya samun rikici irin na Boko
Haram. Mr Campbell, wanda mamba ne a majalisar huldar
jakandancin Amurka, ya ce idan Sheikh Ibrahim El-
Zakzaky ya mutu a hannun gwamnati to "komai zai
iya faruwa a kasar". Sama da shekara biyu kenan gwamnatin
Muhammadu Buhari na tsare da Sheikh Zakzaky da
matarsa a wani kebabban wuri da ba a bayyana ba,
duk da cewa kotuna da dama sun bayar da belinsa. A watan da ya wuce ne gwamnatin jihar Kaduna ta
tuhumi malamin tare da wasu mutum uku da
laifuka takwas ciki har da kisan wani soja a
shekarra 2015, lamarin da suka sha musantawa. Sojan mai mukamin kofaral na cikin ayarin da ke
tare da Hafsan Sojin kasa Janarar Tukur Burutai
lokacin da suka yi arrangama da 'yan shia a garin
Zaria a ranar 12 ga watan Disamba na shekarar
2015. Daga bisani kuma sojoji sun kai wa jagoran 'yan
Shi'a hari a gidansa da ke Zaria inda suka kashe
mutum sama da 300. Sai dai magoya bayan malamin sun ce mutanen da
aka kashe musu sun doshi 1,000, sannan aka yi
awangaba da wasu da dama.
Tsohon Jakada Campbell ya ce 'yan Shi'a a Najeriya
"sun yi kama da Boko Haram ta fuskar kafa
gwamnati". "Mun ga yadda gwamnatin kasar Iran ta nuna
rashin jin dadinta lokacin da aka kama Zakzaky. Ba
mu sani ba ko kasar na tallafawa 'yan Shi'ar
Najeriya da kudade" in ji shi. Mun san yana tsare ne a hannun gwamnatin
tarayya. Ya kara da cewa "gwamnatin na cewa ba za ta sake
shi ba har sai gwamnatin jihar da ya sabawa ta
yanke shawara, wato kenan gwamnatin jiha ce
take tuhumar El-Zakzaky ba ta tarayya ba". Me zai faru idan ya mutu a hannun gwamnati? Mr Cambell ya bayanna wasu abubuwa biyu da ya
nemi gwamnatin Najeriya ta aiwatar domin shawo
kan matsalar tun kafin ta gagari kundila. Abu na farko shi ne gwamnatin Najeriya ta tabbatar
Zakzaky da matarsa sun sami kulawar likitoci sosai
saboda idan ya mutu a hannun gwamnati, "to babu
wanda zai iya cewa ga abun da zai biyo baya". Masanin diflomasiyyar ya ce abu na biyu shi ne
gwamantin tarayya ta ja hankalin gwamnatin jihar
Kaduna da ta bayar da belin Zakzaky, sai kuma a
jira a ga abun da shari'a za ta yi. Gwamnatin jihar Kaduna ta bayanna kungiyar ta
IMN a matsayin haramtaciyya kuma ta hanata
gudanar da taruka. A farkon watan da ya gabata ne magoya bayan
Sheikh Zakzaky suka fara zanga-zanga cikin
lumana a kowace rana inda suka nemi a sako mu
su jagoran nasu. Sai dai sun sha ruwan hayaki mai sa hawaye daga
jami'an tsaro wadanda suka zarge su da ta tada
fitina, zargin da suka musanta.
.
Source @bbchausa
COMMENTS