Blog Archive

Powered by Blogger.

Kalaman Buhari kan wutar lantarki sun jawo ce-ce-ku-ce A Nigeria

'Yan Najeriya suna ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu game da kalaman da Shugaban kasar Muhammadu Buhari kan wutar lantarki a jawabinsa ...


'Yan Najeriya suna ci gaba da bayyana
ra'ayoyinsu game da kalaman da Shugaban
kasar Muhammadu Buhari kan wutar lantarki a
jawabinsa na ranar Dimokradiyya. Shugaban ya ce an samu ci gaba ta fuskar samar da
hasken wutar lantarki yayin da yake yi wa 'yan
kasar jawabi a ranar Talata, wato ranar da
gwamnatinsa ta cika shekara uku a kan mulki. "'Yan Najeriya suna ba da labarin yadda wutar
lantarki ta inganta da kuma yadda suka rage
amfani da janareto," in ji shugaban. Har ila yau ya ce a halin yanzu kasar tana samar da
"MegaWatt 7,500"- an samu ci gaba daga MegaWatt
5,222.3 wanda ta samar a watan Disambar 2017. BBC ta samu dimbin ra'ayoyin jama'a a shafukan
sada zumunta bayan mun bukaci sanin ra'ayinsu
game da ikirarin shugaban a shafinmu na Facebook. Da gaske ne an samu ci gaba game da wadata 'yan Najeriya da hasken wutar lantarki kamar yadda Shugaba Buhari ya yi ikirari a jawabinsa na ranar Dimokradiyya. bbchausa.com Posted by BBC Hausa on Tuesday, 29 May 2018 Yayin da wasu 'yan kasar suka musanta ikirarin
shugaban, wasu kuma sun gasgata ikirarin
shugaban. Asy Kano:"Toh ni dai gani a gidana babu wutar lantarki tun safe, har zuwa yanzu tara na dare..
Dama mun Saba sai 12 dare suke kawowa su
dauke 3 ko 4 na asubahi. Dole muke neman fetur
domin mu tayar da inji saboda azumi ga kuma yara
kanana basa iya barci saboda zafi ..mu dai kam
bamu ga wata ci gaba ba akan harkar wutar lantarki a Najeriya." Amma Zubairu Bello gasgata kalaman shugaban ya yi: "Kwarai kuwa, zancen Shugaba Buhari gaskiya ne. An samu ci gaba a bangaren wutar lantarki. Kuma
ina fatan kamfanin wutar lantarki ya koma
karkashin ikon gwamnatin tarayya a maimakon
'yan kasuwa." Godiya Markus kuma cewa ya yi: "A gaskiya mu har yau babu wani canji dangane da wutar lantarki.
Mu a Tafawa-Balewa da ke jihar Bauchi mun manta
ranar da aka kawo wutar lantarki.Yanzu haka a
babban asibitin gwamnati na kwana, amma sai
yawan sauro. Kai ko dakin ajiye gawa janareta ake
amfani da shi." Amma Suleiman Issa ya ce a inda yake suna samun wuta: "Wannan gaskiya ne saboda a nan Lagos a inda
nake zama a Opebi a Ikeja. Yau fiye da mako daya a
wuni da wuta a dauke wuta sau daya, kafin ka ta
da janarato an kawo wutar saboda haka duk
wanda ya ce ba'a samu cigaba ba sai dai ko ta wani
fannin daban. Ga sauran wadansu ra'ayoyin jama'a - kuma za ku
iya bayyana ra'ayoyinku a shafin namu na Facebook:
.
Source @bbchausa

COMMENTS

Name

Al'ajabi,13,Android zone,69,Applications,3,Aure,25,Blogger zone,1,computer zone,4,Dadin Kowa sabon salo,27,Facebook zone,12,Free Browsing,2,Hausa Films,1,Hausa novels,1,hotuna,2,Java zone,15,Kannywood,55,kiwon lafiya,35,Mata,12,Musics,24,Network,21,News,146,others,16,siyasa,81,Soyayya,3,Symbian zone,5,Video clips,33,video tutorials,3,Whatsapp,1,
ltr
item
Ameer: Kalaman Buhari kan wutar lantarki sun jawo ce-ce-ku-ce A Nigeria
Kalaman Buhari kan wutar lantarki sun jawo ce-ce-ku-ce A Nigeria
dailypost.ng/wp-content/uploads/2018/05/President-Muhammadu-Buhari.jpg
Ameer
https://ameeryau.blogspot.com/2018/05/kalaman-buhari-kan-wutar-lantarki-sun.html
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/2018/05/kalaman-buhari-kan-wutar-lantarki-sun.html
true
2994989324915487916
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy