A kokarin da Hukumar Hisba ta Jihar Kano ke yi na ganin al’ummma na biyayya ga dokokin Allah, a jiya Alhamis daya ga watan Ramadan wanda gal...
A kokarin da Hukumar Hisba ta Jihar Kano ke yi na ganin al’ummma na biyayya ga dokokin Allah, a jiya Alhamis daya ga watan Ramadan wanda galibin al’ummar Musulmi a fadin duniya suka fara aiwatar da daya daga cikin rukunan Musulunci na zumi ta damke Gandaye wadanda suka keta alfarmar watan. Tun da farar safiyar ranar rundunar Hisban ta kai samame domin damke Gandayen a Unguwar Sabon gari da wasu sassa na Jihar Kano da ake gudanar da kasuwar tsaye. Tawagar Jami’an Hisbar sun yiwa wasu layukan Sabon Gari dirar Mikiya, wanda hakan ya ba su sa’ar cika hannu da Gandaye Goma maza da kuma mace guda daya. Wakazalika, daga Sabon Garin, jami’an Hisba a karkashin jagorancin Muhammad Tasi’u Muhammad suka nausa zuwa Unguwar Fagge inda masu irin wannan halin suka tsere ba a samu damke ko guda daga cikinsu ba.
Da yake karin haske ga manema labarai, Babban Darakta Hukumar Hisba ta Jihar Kano, Malam Abba Sa’id Sufi ya jinjina wa jami’an da aka dora wa alhakin damke Gandayen bisa wannan kokari wanda ya ce ba abin mamaki ba ne idan aka yi la’akari da zakakuran ma’aikatan hukumar. Daga ya yi doguwar nasiha ga masu irin wannan hali da cewar su ji tsoran Allah, ya kuma tabbbatar masu da cewa duk inda suka buya Allah na ganinsu. A karshe Abba Sufi ya taya al’ummar musulmi murnar shiga wannan wata mai alfarma tare da yin addu’ar Allah ya karbi ibadunmu. Hakazalika Sufi ya jijinawa Gwamna Ganduje bisa fitar da miliyoyin Nairori domin ciyar da marasa galihu a Jihar Kano .
Source @leadershipayau
COMMENTS