Wata kotu a jihar Ekiti da ke kudu maso yammacin Najeriya, ta yankewa wani mutum hukuncin kisa ta hanyar rataya, bisa laifin satar kwalaban ...
Wata kotu a jihar Ekiti da ke kudu maso
yammacin Najeriya, ta yankewa wani mutum
hukuncin kisa ta hanyar rataya, bisa laifin satar
kwalaban giya bakwai da kuma kwalin taba
sigari daya. A yayin yanke hukuncin da aka yi a ranar Laraba,
alkalin babbar kotun ya samu mutumin da laifin
fashi da kuma mallakar makamai da suka hada da
adda da kuma gatari a yayin da ya je satar
abubuwan. Mai gabatar da karar na rundunar 'yan sandan jihar
ya ce, mutumin da aka yankewa hukunci wato Raji
Babatunde, na daga cikin wadansu gungun barayi
hudu da suka yi fashi a wasu gidaje da ke Ado Ekiti. Bayan fashin da suka yi na satar kwalaban giyar da
kwalin tabar, mutumin da sauran abokan fashin
nasa sun yi wa wani mutum fashin wayoyin salula
kirar Nokia da kuma Techno.
.
Source by bbchausa
COMMENTS