Ana zargin wani matashi mai suna Aliyu Aminu wanda aka fi sani da Haidara, mai kimanin shekara 17 sha bakwai da kashe abokinsa mai suna Aliy...
Ana zargin wani matashi mai suna Aliyu Aminu
wanda aka fi sani da Haidara, mai kimanin shekara
17 sha bakwai da kashe abokinsa mai suna Aliyu
Shehu mai shekara 17 da suke zaune a unguwa
daya a sanadadiyyar cacar baki a tsakaninsu da
kuma zugar abokai. Lamarin ya faru ne a ranar Talatar da ta gabata da
misalin karfe tara na safe, a Unguwar Gangaren
Kwadi da ke Tudun Wadan Zariya a Jihar Kaduna. Wakilinmu wanda ya ziyarci unguwar ya yi kokarin
jin ta bakin iyayen marigayin amma sun ce ba za su
ce komai ba saboda ba su a wurin da abin ya faru.
Haka iyayen wanda ake zargin da kisan, sun ki
cewa komai, illa suna nuna rashin jin dadinsu da
nuna juyayi a kan abin da ya faru. Aminiya ta samu labarin wadansu sun yi kokarin
raba samarin, amma saboda abokai suna zuga su
kuma ajali na kira sai da suka fafata a tsakaninsu
inda daya ya kashe daya. Wata majiya ta ce marigayi Aliyu Shehu ya ce wa
wanda ya kashe shi Aliyu Haidara zai tura
abokansa domin su yi maganinsa idan ya ci gaba
da yi masa gani-gani. Shi kuma Haidara sai abokai
suka ce masa idan ba ka tsaya ka nuna masa cewa
bai isa ba, to wannan fadan ba zai kare ba, duk inda ya gan ka sai ya nuna maka raini, don haka ka
tsaya ka yi maganinsa. Majiyar ta ce hakan ne ya sa suka zaga bayan gari
suka je wani fili da ake kira filin Sale Maidoki da
wadansu ke kira da filin Alaliya domin su goge
raini, a nan ne suka harde da kokowa, inda Aliyu
Haidara ya dauki marigayi Aliyu Shehu ya doka
kansa a kasa, wanda haka ya yi sanadiyar karyewar wuyansa, daga nan ne aka dauke shi
zuwa gida, aka wanke masa raunin da ya samu a
keyarsa, ana shirin kai shi asibiti sai aka ji ya yi wani
irin numfashi, daga nan sai rai ya yi halinsa. Majiyar ta ce an sanar da ’yan sanda abin da ya faru,
suka zo da mota suka dauki gawar suka kai asibiti
inda aka tabbatar da rasuwarsa, sannan aka dawo
aka ba iyayen gawar domin yi masa jana’iza. Kuma
wadanda suka yi masa wanka sun ce wuyansa ne
ya karye wanda hakan ya yi ajalinsa. Wata majiya a unguwar ta shaida wa wakilinmu
cewa iyayen wanda ya yi kisan sun yi kokarin
ziyartar gidan su marigayi domin yi ta’aziyya da
jajanta musu, amma sai iyayen marigayin suka ki
yarda su matso kusa da inda suke, suka hau su da
hargowar cewa ba za su taba yarda su kyale wannan abu da ya faru ba. Babban Jami’in ’Yan sandan Tudun Wada, Zariya,
ASP Abdullahi Yusuf ya tabbatar da faruwar lamarin
inda ya ce yaron da ake zargi da kisan ya gudu,
amma sun gayyaci mahaifinsa da shaidu, domin
tattara bayanai, kuma sun baza komarsu domin
farauto wanda ake zargi da kisan.
.
Source @aminiya
COMMENTS