Akalla mutane shida ne suka hallaka a wani harin kunar bakin wake da aka kai wani masallaci a garnin Bama, a jiahr Borno da ke arwa maso gab...
Akalla mutane shida ne suka hallaka a wani
harin kunar bakin wake da aka kai wani
masallaci a garnin Bama, a jiahr Borno da ke
arwa maso gabashin Najeriya.
.
Mutanen da suka mutu sun hada da mahara biyu
mace da namiji, da kuma masallata hudu. Shugabar hukumar bada agajin gaggawa ta jihar
Borno Ya Bawa Kolo ta shaidawa BBC cewa wasu
mutanen kuma sun ji rauni, kuma tuni aka garzaya
da su asibiti. Hukumomin jihar sun ce an kai harin ne lokacin da
ake sallar asuba
Kawo yanzu babu wanda ya dauki alhakin kai
harin, amma dai kungiyar Boko Haram tana yawan
kai irin wadannan hare-hare a yankin. Hukumomin Najeriya na ikirarin samun galaba a
kan kungiyar Boko Haram, to sai dai kungiyar na ci
gaba da kai hare-hare a wasu yankunan arewa
masu gabas, musamman ma a jihar Borno. Rikicin Boko Haram ya janyo mutuwar dubban
mutane a Najeriya gami da raba sama da mutum
miliyan biyu da mahallansu.
.
Source by @bbchausa
COMMENTS