Mutane fiye da (2.7 million) milyan biyu ne a yammacin Turai rikicin ganin asirin masu amfani da shafin Facebook ya shafa. An bayyana haka ...
Mutane fiye da (2.7 million) milyan biyu ne a
yammacin Turai rikicin ganin asirin masu amfani
da shafin Facebook ya shafa. An bayyana haka ranar Juma’a ne wanda ita
nahiyar Turan tayi, inda take cewar zata bukaci
wasu amsoshi daga jagorar abubuwan da ake
amfani dasu ta, hanyar sadarwa ta zamani. ‘’Facebook ya tabbatar da cewar ana amfani da
dama (data) ta amfani da hanyar sadarwa ta
zamani, ta mutanen da suka fi milyan biyu, ta
hanyar da bata kamata ba,an rarraba da
Cambridge Analytica, wani mai magana da yawun
kamfanin Christian Wigand shi ya bayyanawa kamfanin dillancin labarai na Reuters’’. Facebook ya yarda da an aikata laifin, amma
kuma ‘’Ta hanyar da bata kamata ba’’ na (data )
dama ta amfani da wata kafar sadarwa ta zamani,
a yammacin Turai, an dai bada sanarwar ranar
Juma’a, cewar zata bukaci amsoshin wasu
tambayoyin da zasu yi. Tarayyar Turai ta rubutawa Facebook makon
daya wuce, domin ta tambayi ko Turawa
yammacin Turai nawa ne, abin ya shafa, na
laifukan da ake aikatawa ta satar (datar) masu
amfanin da hanyoyin sadarwa na zamani, wajen
rarraba ita datar, da wani kamfanin kwararru mai suna Cambridge analytica, mai bada shawara
akan harkokin siysa. Kwamishinan harkokin shari’a na nahiyar Turai
Bera Jouroba shi zai magana da babban jami’in
gudanarwa na Facebook, Sheryl Sanberg, farkon
mako mai zuwa, domin a tattauna matakan da za
a dauka, domin samun maslaha akan laifin da
aka aikata. Ya yi karin bayani kamar haka’’ Za muyi nazarin
wasikar da muka samu daga (Facebook),
dukkan abub uwan da take magana akan su,
amma kuma maganar gaskiya ita ce, wannan zai
biyo bayan wasu tarurrukan, da za ayi da
Facebook.’’ Shugaban kamfanin Facebook Mark Zuckerberg
ranar Alhamis ya bayyana cewar akwai mutane
milyan 87 aduniya wadanda, ita wannan cuwa-
cuwa ko kuma badakala ta rarraba datar mutane
gawasu, wannan kuma ya sa kamfanin shiga
wani rikici, wannan kuma shi yasa aka fara tababar yadda za a iya kare data mutane nan
gaba. Ita dai nahiyar Turan tana kokari ne ne
kaddamar da yadda za arika kare datar masu
amfani da kafofin sadarwa na zamani, za kuma a
bullo da wasu dokoki, a karkashinsu shi kuma
shi kamfanin , za a iya cin tarar shi ta kashi hudu
cikin dari, na kudaden da suka samu a shekara, saboda yadda aka karya ka’idojin
.
Source by hausaleadership
COMMENTS