Wata Matashiyar yar Najeriya yar asalin jihar Katsina Hajiya Fadila Sani Tilo, ta mayar da martani ga kalaman shugaban Najeriya Muhammadu Bu...
Wata Matashiyar yar Najeriya yar asalin jihar
Katsina Hajiya Fadila Sani Tilo, ta mayar da martani
ga kalaman shugaban Najeriya Muhammadu
Buhari inda yace mafi yawan Matasan Najeriya
cima zaune ne malalata ita kuma ta ce matasan ba
cima zaune bane. Hajiya Fadila Sani Tilo, ta bayyana hakan ne a
lokacin da take zantawa da LEADERSHIP A ranar
Lahadi, cewa kamata ya yi a jinjinawa matasan
musamman yan arewa saboda yadda suke fadi
tashin neman na kansu domin duk wani lungu
da sakon da kabi zaka ga matasa sun tashi suna neman yadda za su tsira da mutuncin su. A cewar ta yanzu a arewacin Najeriya duk inda ka
shiga za kaga matasa na tura baro wasu na
Baban Bola wasu na Tura ruwa da sauran
nau’ukan aikin karfi dan neman halak din su to a
na menene za’a kira matasan da cewa su cima
zaune ne su. Kasancewar Muhammadu Buhari shugaban kasa
watakila batun da ya yi wasu tsiraru ya gani irin
masu macecciyar zuciyar nan da suke bin kan
’yan siyasa wadanda ba za’a rasa ba suke bangar
siyasa ya furta wannan kalamai akan su idan
haka ne kuma bai kamata ya yi jam’i yace matasan Najeriya malalata bane kuma cima zaune
ba. Hajiya Fadila Sani, tace idan irin wannan aikin da
matasan ke yi na karfi bai gamshe shi ba to ya
samar musu da aikin da ya dace tunda a lokacin
da yake yakin neman zabe a shekarar 2015 ai ya
bayyana cewa zai samarwa da matasan aikin yi
me ya hana ya cika wannan alkawarin yanzu har ya ke kiran matasan da Malalata. Ta kuma yi kira game da bai wa shugaban kasa
Muhammadu Buhari, shawarin cewa idan ba zai
iya samarwa da matasan nan ayyukan da za su yi
ba kar ya kira su cima zaune domin wani ma
sana’ar faci ya ke yi wani Makanikanci da haka
kuma yake rike da iyalansa wanda da basa wannan sana’ar da su ne zai sa a kirasu cima
zaune amma ta ya ya mai sana’a ko wanda yake
da aikin yi za’a kira su malalata. Haiya Tilo, ta kara da cewa watakila matasan da
shugaban kasa Buhari ya ke kira malalata din irin
wadancan yan bangar siyasar ne da suka kashe
zuciya suke bin kan yan siyasa wanda kuma duk
yadda kayi da samarwa mutane aikin yi wasu ba
za su yi saboda sun saba da karbar na banza. Sannan ta ce a dangane da wannan kalaman na
shugaba Buhari na kiran matasa cima zaune ya
sake komawa kafar yada labarai ya bai wa
matasan hakuri saboda ya wanke kansa dan a
gaskiya matasa ba malalata bane kamar yadda
yake fadi. Daga nan sai Hajiya Fadila Tilo, tace saboda yadda
matasan Najeriya ke jajircewa wajen neman na
kansu da fadin tashin da suke yi dan rufawa
kansu asiri kamata ya yi gwamnati ta bai wa
matasan lambar yabo, domin baya ga sana’aoi da
suke ai shi Buharin ya sani a lokacin sa ne matasan da dimbin yan Najeriya suka koma
gona.
.
Source @hausaleadershi
COMMENTS