Blog Archive

Powered by Blogger.

Yau Shekara hudu da sace 'yan Matan Chibok

A ranar 14 ga watan Afrilun shekarar 2014 ne mayakan Boko Haram suka sace 'yan mata 'yan sakandaren Chibok sama da 200 a garin Chibo...



A ranar 14 ga watan Afrilun shekarar 2014 ne
mayakan Boko Haram suka sace 'yan mata
'yan sakandaren Chibok sama da 200 a garin
Chibok da ke arewa maso gabashin Najeriya. Sama da 100 daga cikin 'yan makarantar da ake wa
lakabi da 'yan Matan Chibok ne wala'allah suka
tsere daga 'yan Boko Haram don radin kansu da
wadanda dakarun kasar suka kubutar ta hanyar
tattaunawar gwamnati da masu shiga tsakani. Kungiyar Bring Back Our Girls na daga cikin
wadanda suka fara gangamin matsin lamba ga
gwamnnatin shugaba GoodLuck Jonathan da aka
sace 'yan matan a lokacin mulkinsa, dan kubutar
da su. To amma an dauki lokaci har bayan shudewar
gwamnatin Jonathan din babu wata ko daya daga
cikin 'yan matan da aka kubutar. A lokacin mulkin shugaba Buhari sojojin Najeriyar
suka yi kicibis da daya daga cikin 'yan matan mai
suna Amina Nkeke dauke da jaririyar da ta haifa
bayan auren da ta yi da daya daga cikin mayakan
da suka sace su. A iya cewa sannu a hankali, tun daga bayyanar
Amina sai hanya ta bude kuma ba a jima ba sai
kungiyar Boko Haram, ta dinga fitar da bidiyon da
ke dauke da 'yan matan na Chibok da kungiyar ta
sace. Bidiyon da ya fi daga wa gwamnati da iyayen yaran
hankali, shi ne wanda ya nuna daya daga cikin
matan sanye da shudin hijabi da farin nikabi,
kewaye da wasu matan su kusan goma, tana
magana. Daya daga cikinsu, wacce ta yi jawabi a cikin
bidiyon, ta ce ba za su koma wurin iyayensu ba. Ta
yi kira ga iyayensu da su tuba, su yi mubaya'a ga
kungiyar. Sannu a hankali, adadin 'yan matan da aka kubutar
da wadda aka tsinta suka tasamma sama da 100,
sai dai har yanzu da aka cika shekara hudu cif da
sace su wasu da dama ba a kubutar da su ba. Boko Haram tana kai hare-hare a arewa maso
gabashin Najeriya ne tun shekarar 2009, kuma ta
kai hare-hare kasashe masu makwabtaka. Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutane sama da
20,000 rikicin na Boko Haram ya hallaka, yayin da
wasu dubbai suka yi hijira zuwa kasashe makofta.
Wasu sama da miliyan daya ke jibge a sansanonin
'yan gudun hijira a ciki da wajen Najeriya.
.
Source by @bbchausa

COMMENTS

Name

Al'ajabi,13,Android zone,69,Applications,3,Aure,25,Blogger zone,1,computer zone,4,Dadin Kowa sabon salo,27,Facebook zone,12,Free Browsing,2,Hausa Films,1,Hausa novels,1,hotuna,2,Java zone,15,Kannywood,55,kiwon lafiya,35,Mata,12,Musics,24,Network,21,News,146,others,16,siyasa,81,Soyayya,3,Symbian zone,5,Video clips,33,video tutorials,3,Whatsapp,1,
ltr
item
Ameer: Yau Shekara hudu da sace 'yan Matan Chibok
Yau Shekara hudu da sace 'yan Matan Chibok
http://fm.nextwapblog.com/files/6475/chibok.png
Ameer
https://ameeryau.blogspot.com/2018/04/yau-shekara-hudu-da-sace-matan-chibok.html
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/2018/04/yau-shekara-hudu-da-sace-matan-chibok.html
true
2994989324915487916
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy