Blog Archive

Powered by Blogger.

Akalla mutum miliyan sittin da uku ne a Najeriya basa samun isashshen barci a kowacce rana.

Bincike ya nuna akalla mutum miliyan sittin da uku a Najeriya ne basa samun isashshen barci a kowacce rana. Likitoci sun ce da dalilan da ka...


Bincike ya nuna akalla mutum miliyan sittin da uku a Najeriya ne basa samun isashshen barci a kowacce rana. Likitoci sun ce da dalilan da kan jawo rashin wadataccen bacci sun hada da rashin ayyukan yi, da tsadar rayuwa da matsalolin kasuwanci, da rashin tsaro, da hidimomin iyali da kuma rashin kwanciyar hankali a wuraren aiki ko cikin al'umma. Wasu mutanen ba sa bacci kuma ba su fara kafa hira sai a lokacin da dare ya yi, kuma sukan kwashe tsawon lokaci suna hirar akan al'amurra daban-daban har safiyar Allah. Bincike ya nuna akwai dalilai ma su yawa da ke hana mutum samun isasshen bacci, watakila a sabili da damuwa ko kuma zumudin wani abu ko kuma rashin samun koshin lafiya. Duk da cewa wasu mutanen sun san da cewa akwai illar da ke tattare da rashin samun cikakken bacci amma suna ci gaba da yin hira mai tsawo da dare. To ko me likitoci ke cewa? Bacci kamar yadda likitoci suka nuna wani abinci ne da dan adam kan bai wa jikinsa kuma wata hanya ce ta gina lafiyar kwakwalwa da samun koshin lafiya. Dakta Hassan kwararren likita ne a Najeriya, ya gargadi masu kwashe tsawon dare ba sa bacci da su dinga takaita hira mai tsawo musanman a lokacin da jiki ke bukatar hutu. Dakta Hassan ya ce '' Samun bacci alamu ne na samun koshin lafiya ga bil'adama. Duk mutumin da ba ya samun isasshen bacci - to zai iya kamuwa da hawan jini. Wadda a sakamakon haka zai iya kamuwa da wasu cututtuka.'' Ya kara da cewa ''Ana kiran rashin samun wadataccen bacci insomania- kuma in ciwon insomania ya yi yawa yakan haifar wa mutum aikata wasu abubuwa kamar na mai tabin hankali. Wannan ne ya sa ake bukatar mutum ya samu bacci a tsawon sa'o'i shida zuwa takwas." Wadansu matasa da wakilinmu Umar Shehu Elleman ya yi hira da su a birnin Legas sun fada ma sa cewa sukan kwashe tsawon dare suna hirar siyasa da matsalolin da ke damunsu. Sun ce bayan gari ya waye sukan yi baccin sa'o'i biyu zuwa uku ne kadai, sannan su tafi wuraren aiki. Bincike ya nuna wasu daga mutane na shan kwayoyi da za su hana su yin bacci a tsawon dare. A kasashe kamar Japan da Saudi Arebiya da Philliphine da Sweden da kuma Indiya mutane ba sa wuce tsawon sa'o'i shida suna bacci. To amma a kasashe kamar Birtaniya da Finland da New Zealand akalla suna samun tsawon bacci kamar na sa'o'i bakwai da rabi a kowanne dare. A Afirka babu wani takamaiman tsari ko tsawon sa'o'i a mtasayin alkalumman da za a dogara da su na bacci tsakanin kasashe. Sai dai an tabbatar da cewa matsalolin rayuwa da ke tattare da al'ummar nahiyar za su zama kadan daga dalilan rashin samun wadataccen bacci. . Source @ bbc hausa

COMMENTS

Name

Al'ajabi,13,Android zone,69,Applications,3,Aure,25,Blogger zone,1,computer zone,4,Dadin Kowa sabon salo,27,Facebook zone,12,Free Browsing,2,Hausa Films,1,Hausa novels,1,hotuna,2,Java zone,15,Kannywood,55,kiwon lafiya,35,Mata,12,Musics,24,Network,21,News,146,others,16,siyasa,81,Soyayya,3,Symbian zone,5,Video clips,33,video tutorials,3,Whatsapp,1,
ltr
item
Ameer: Akalla mutum miliyan sittin da uku ne a Najeriya basa samun isashshen barci a kowacce rana.
Akalla mutum miliyan sittin da uku ne a Najeriya basa samun isashshen barci a kowacce rana.
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEjIjDNmEF_9HJ6HU0IP7rbSJ8eQMGgw0Gbwts2LccpMNTLtlmoa1llYz03G7gYz7J1uAoLYPmu4wEvRS_AZdGmmm_1h8NGAOyGVmzFBgPLjo2Ol3MsPQIxxXZrvQxZQ1EGLzYaZ6SjL2JWO/s320/Sleeping.jpg
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEjIjDNmEF_9HJ6HU0IP7rbSJ8eQMGgw0Gbwts2LccpMNTLtlmoa1llYz03G7gYz7J1uAoLYPmu4wEvRS_AZdGmmm_1h8NGAOyGVmzFBgPLjo2Ol3MsPQIxxXZrvQxZQ1EGLzYaZ6SjL2JWO/s72-c/Sleeping.jpg
Ameer
https://ameeryau.blogspot.com/2018/04/akalla-mutum-miliyan-sittin-da-uku-ne.html
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/2018/04/akalla-mutum-miliyan-sittin-da-uku-ne.html
true
2994989324915487916
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy