Jiya a babban birnin tarayya Abuja, ‘yan zanga zangar ‘yan kungiyar ‘yan uwa musulmi a Najeriya (IMN) suka yi rikici da jami’an ‘yan sanda n...
Jiya a babban birnin tarayya Abuja, ‘yan zanga
zangar ‘yan kungiyar ‘yan uwa musulmi a
Najeriya (IMN) suka yi rikici da jami’an ‘yan sanda
na Najeriya da sauran wasu jami’an tsaro. Yan
kungiyar da aka fi sani da Shi’a, wadanda ke
kusa da manyan titunan birnin Abuja tun makon da ya wuce, suna nuna rashin amincewarsu da ci
gaba da tsare shugaban su, Sheik Ibrahim El-
Zakzaky, wanda yake tsare a hannun jami’an
tsaro (DSS). Wasu da abin ya faru a gaban su sun fada wa
LEADERSHIP cewa jami’an tsaron sunyi iya
kokarin su dan kar lamarin yakaiga an yiwa
mutane mummunan rauni. “A cewar su, ‘yan
Shi’ar suna jifan motar jami’an tsaron da dutsuna
da kuma sandunan. Yan Shi’ar ba su gujewa barkonan tsohuwar da
jami’an tsaron suka harba dan su suka kore su,
“in ji daya daga cikin wanda ya zanta da manema
labaran. Kakakin rindinar yan sandan, DSP Anjuguri
Manzah, yace ‘yan kungiyar Shi’a sun ji wa ‘yan
sanda 22 rauni a lokacin zanga-zangar. Manzah
ya kara da cewa, hukumar ‘yan sandan birnin
tarayya sun sake mayar da hankali a wasu sassa
na Maitama bayan tashin hankali da ‘yan kungiyar Shi’ar (IMN) suka yi.Yan zanga zangar
sun lalata wasu motocin gwamnati dana ‘yan
sanda sa’annan ‘yan kungiyar Shi’ar sun jikkata
’yan sanda 22 a lokacin zanga-zangar. Manzah
yace ‘yan sanda kuma sun kama ‘yan zanga-
zangar guda 115, inda suka kama su da dankuna , sanduna, karafen rodi da kuma
duwatsu daga gare su. Wadanda ake tuhuma za
a gurfanar da su gaban kotun bayan an kammala
bincike. Hukumar ‘yan sandan birnin tarayya ta
gargadi ’yan kungiyar Shi’a da su guji yin duk
wani abu da zai iya haifar da rashin zaman lafiya. Haka kuma ya bukaci jama’a musamman ma
iyaye kada su bari ‘ya’yansu su kasance ana
amfani da su wajen tashin hankali ko duk wata
zanga-zangar zata iya haifar da rashin zaman
lafiya da kwanciyar hankalin jama’a.
.
Source, by leadershipayau
COMMENTS