Wata ‘yar shekara sha shida mai suna Emani Kure ta aikata aika-aika sakamakon hallaka mahaifinta har lahira. Emani Kure wadda take da zama d...
Wata ‘yar shekara sha shida mai suna Emani Kure
ta aikata aika-aika sakamakon hallaka mahaifinta
har lahira. Emani Kure wadda take da zama da iyayen a
kauyen Karaban dake yankin Bwari a garin
Abuja ta kashe mahaifin nata dan shekara 40 mai
suna Kusha Kure,inda ‘yan sanda suka tabbatar
da cewar, lamarin ya auku ne a ranar Lahadin
data gabata da misalin karfe uku na dare. Yarinyar ta hallaka mahaifin nata ne saboda yaki
amincewa bukatar ta na auren wani saurayin ta
mai suna Nasiru Musa. Emani da masoyin nata Nasiru Musa, sun shafe
kimanin shekaru biyu suna soyayayya sun
bayyana ra’ayin su na son yin aure. Kwamishinan rundunar ‘yan sanda na Abuja
Sadik Bello ya bayyana cewar, an kawo rahoton
lamarin ga ofishin ‘yan sanda na gudumar Bwari. Ya ci gaba da cewa, jami’an sa masu na sashen
binciken kisan kai, sun cafko Emanu tare da
mahaifiyar ta mai suna Asabe Kure, wadda ake
zargin ta taka muhimmiyar rawa wajen kashe
mijin nata. Ya kara da cewa daga baya an mayar da binciken
ga sashen binciken kisan kai dake rundunar. A hirar da manema labarai suka yi da wadda ake
zargi Emani, ta yi bayani mai girgizarwa akan
yadda ta sheka da mahaifin nata barzahu. Emani ta ce, “na kashe mahaifi na saboda yaki
amincewa in auri masoyi na Nasiru Musa.” Acewar ta, “ mun sahfe shekaru biyu muna
soyayya, kuma mahaifi na ya sha jibga ta a lokuta
da yawa akan in janye ra’ayi na son auren
Nasiru”. Emani ta kara da cewa, na kashe shine da
misalain karfe uku na dare kuma mahaifiya ta ce
ta bani wannan shawarar a lokacin da muke
kwance a harabar gidan mu, cewar in shiga daki,
inda mahaifi na ke yin barci in kashe shi. Ta umarce in yi amfani da adda don in hallaka shi,
inda naje inda yake ajiya addar sa na dauko naje
dakin sa na kashe shi. Ta ce, “na sassare shi a wuyan sa,bayan da
mahaifiya ta rike mini kafar sa.” A cewar ta, “bayan na kashe shi, na gudu daga
gidan mu zuwa gidan kawa ta mai suna Regina. Ta ce, Nasiru bai da masaniyyar ina son in kashe
mahaifin nawa, kuma shi ma ya kidime a lokacin
da ya samu labarain abinda na aikata.” A na ta bangaren, mahaifiyar ‘yar shekara talatin
da biyar ta karya zargin da ‘yarta ta dora mata. Asabe ta ce,”nida majina marigayi bama goyon
bayan Emani akan son da take na auren Nasiru
Musa, amma tayi biris da jan kunnen da muka yi
mata” . A cewar ta, a lokacin mijina yana barci a daki
kuma ‘yar karamar yata da nake goyo ta tashi ta
fara kuka na tashi don in bata Nono tasha, sai
kawai naji mijina yana ihu a cikin dakin sa, inda
nayi gaggawa na kirawo siriki na mahaifin mijina. Shi da sauran jama’a suka shigo gidan mu suka
iske mijina a cikin jini, kuma yata bata wurin,
domin ta gudu. Acewar ta, na fara zargin ta da Nasiru Musa a
zaman wadanda suka aikata ta’asar. Ta ce, munje ofishin “yan sanda na gudunduma
dake Bwari don kai rahoton akuwar lamarin,
inda na sheda masu cewar, ina zargin ‘yata da
saurin ta akan aikata ta’asar, inda daga baya ‘yan
sanda suka cafko Nasiru da ‘yata kuma ta amsa
laifin ta, amma ta ce wai nice na umarce ta kashe mijin nawa. Nasiru dan shekara ashirin da biyu, ana zaegin sa
da hkda baki don kashe Kure. Nasiru ya ce bai san cewar Emani ta kitsa son
kashe mahaifin ta ba. Har yanzu wadanda ake zargin Emani da
mahaifiyar ta da kuma Nasiru suna tsare ana
gudanar da bincike akan lamarain.
.
Source by leadershipayau
COMMENTS