Blog Archive

Powered by Blogger.

Bunkasar Shehu Inyass Ce Ta Sabbaba Yin Maulidinsa A Abuja Da Kaduna - Sheikh Dahiru Bauchi

An bayyana cewar girman daukaka da kuma bunkasar da Shehu Ibrahim Inyass ya yi a wannan duniyar ce ta sanya a wannan shekarar aka samu damar...



An bayyana cewar girman daukaka da kuma
bunkasar da Shehu Ibrahim Inyass ya yi a
wannan duniyar ce ta sanya a wannan shekarar
aka samu damar yin maulidinsa a manyan
garuruwa biyu na Nijeriya, wato birnin tarayya
Abuja da kuma jihar Kaduna. Shehu Dahiru Usman Bauchi, shi ne ya bayyana
hakan a hirarsa da manema labaru a sa’ilin da ke
warware zare da abawa kan cewar babu wata
barakar da ta kunno kai a cikin Tijjaniyya
dangane da wannan maulidin, taron ‘yan jaridar
wanda ya gudana a gidansa da ke Bauchi a jiya, yana mai amannar cewa miliyoyin jama’a ne suka
hallara a Abuja da Kaduna don yin wannan
maulidin. Ya bayyana cewar Shehu Ibrahim Inyass mutum
ne wanda aka haifa a kasar Senigal ne, an kuma
haifesa sama da shekaru 117 da suka gabata, a
don haka ne ya ce a sakamakon dumbin alkairai
da ya zo da shi ne ya sanya a kowace shekara a
ke tururuwar yin bukukuwan tunawa da ranar haihuwarsa domin nuna godiya wa Allah
madaukakin Sarki, “Rayuwarsa ta bamu alkairai
da daman gaske don haka ne muke taruwa
domin gode wa Allah a bisa samunsa,” In ji Shi.
Tun da fari, ya bayyana cewar sun kira taron
manema labaru ne domin su nuna godiyarsu ga Allah a bisa samun nasarar yin wannan babban
taron na maulidi, hade kuma da nuna godiyarsu
ga wadanda suka dafa tun daga fara taron har ga
zuwa kammalasa, ya bayyana cewar sun ji dadin
yadda aka yi taron lami lafiya ba tare da wata
mummunar matsala ba. Ya ke cewa, “Dukkanin wani abun da ya faru a
yayin wannan babban taron ya kamata a yafe wa
juna, mu dai ba mu yi niyyar bata ma wani ba, ba
mu kuma bawa da kowa ba; wadansu daga cikin
manya da suke yin wani abu wannan ba wani
abun zargi bane, ko nima haka nake, ko kuma haka kuke. Don haka babu wata matsala,
dukkaninmu mun yi ne domin Shehu,” Shehu Dahiru ya ci gaba da cewar da sun so yin
taron ne waje guda, amma hakan ya zo ya fi
karfinsu domin girma daukakar lamarin, “Babu
wani abun zargi a cikin lamarin, da mun tsara
cewar za mu yi taron ne a waje guda daya tak. Sai
kasaitar bunkasar Shehu Ibrahim ita kuma ta ce to bana taron har guda biyu za a yi dole ne a yi
wani a Kaduna da kuma na Abuja, karamarce ta
sanya haka. Da wadanda suka je Abuja da
wadanda suka je Kaduna dukkaninmu mutanen
Shehu ne, kuma soyayyar Shehu ce ta hada mu,”
In ji Malam. Malamin ya kara da cewa yin taro a waje biyun
babu wata doka ko kuma ka’ida daga cikin
kurunnai na shiga darika ko na darika da wani
ya karya don haka babu wata matsala illa nuna
soyayya da kuma bunkasuwar Shehu Inyass. Da yake karyata batun cewar akwai baraka a
tsakaninsu ya ce “ai mu bamu rabuwa, kasaitar
karamar Shehu ce ta ce bana ba a waje daya za a
yi maulidinsa ba; sai dai a yi a gari biyu, kuma ba
a jayayya da karamar yadda taso haka za a yi
dole, karamar ce ta ce lallai ne a yi a Kaduna da Abuja kuma rana daya. Mu ‘yan darika ba mu
rabuwa, abun da ya hada mu da kowa a cikin
darika zikiri da lazumin juma’a kuma dukka babu
wanda aka karya,” Kamar yadda ya bayyana. A ta bakinsa ke cewa, idan mutum ba sai girma
da daukakar Shehu ba, to idan ya ga miliyoyin
jama’an da suka je Abuja zai gane hakan,
“mutum bai san girma da karama ba, ka duba
taron nan da aka yi a Abuja nan, idan mutum ya
gani zai tabbatar da karamar waliyin Allah, Shehu Ibrahim Inyas walihi ne, duk wanda ya gode wa
Allah a sakamakon samuwarsa shi ma ya zama
wani abu a wajen Allah. Irin miliyoyin da suka je
wannan maulidin ko gwamnati ta yi kadan ta tara
jama’a haka nan, amma ka duna karamar Shehu
ta yi ta daukan mutane tana kaisu Abuja don wannan maulidin,” Bai tsaya haka ba, ya kuma kara da nuna
alheninsa ga wadanda suka raunata kasantuwar
dandazon jama’a da suka yi turuwar zuwa taron
kama daga zuwa ko dawowa, ko kuma wadanda
suka samu raunuka a wajen taron, “Duk wanda
ya ji rauni a yayin sa’ayin wannan maulidin muna mika sakon gaisuwarmu garesa da kuma yi masa
addu’ar Allah bashi lafiya, duk wanda ya rasa
ransa (in akwai) muna addu’ar Allah ya jikansa,
sannan kuma jama’anmu gaba daya Allah ya
bada hakuri, ya kuma bamu ladan sa’ayi,” A
cewar Shi. Da yake bayyana dalilinsu na shigo da yin addu’a
wa kasar nan a cikin shakalin taron maulidin na
bana wanda kuma basu saba yin hakan ba,
Dahiru Bauchi ya bayyana dalilinsu “tabbas kasar
tamu tana bukatar addu’a a wannan lokacin
sosai, da ai babu Boko Haram, babu garkuwa da mutane, babu rikici a tsakanin manoma da
makiyaya, babu satar shano, haka babu wani
abun wai Buharin daji dukka babu da. A don
haka ne muka dauki yin addu’a a matsayin hanya
daya domin kawo karshen matsalolin da suka
addabi kasar nan domin ceto kasar Nijeriya,” Kamar yadda ya shaida. Haka zalika Shehu Dahiru Bauchi ya gode wa
tawagar bakin da suka samu halartar wannan
maulidin na bana kama daga jikokin Shehu Inyas
wadanda suka tattako tun daga kasashen waje
da kuma manyan baki da suka hallara a Abuja da
Kaduna domin nuna soyayya ga Shehu Ibrahim “muna godiya wa dukkanin wadanda suka samu
halartar wannan taron, jama’armu na Kaulaha,
‘ya’yan Shehu da Jikokinsa, maza da mata, da
wadanda suka zo daga Moroko, jikokinsa na
kasar Aljeriya, haka kuma da manyan malamai
mukaddamai na Misra da na kasashen Sudan, Amurka da kasashe irin su Nijer da Kamaru da
sauran wuraren da suka zo muka yi musharaka
da su cikin wannan taron, muna godiya Allah ya
saka musu da dukkanin alkairai,”. In ji Shi. Dahiru Bauchi ya kuma yi amfani da taron masu
farautar labaran wajen nuna godiyarsa ga
shugaban Nijeriya Alhaji Muhammadu Buhari a
bisa halartar wannan taron da ya yin a Abuja
wanda ya aiko wakilisa Ministan ilimi, Adamu
Adamu, haka kuma, ya nuna matukar godiyarsa ga gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa’i
a bisa gudunmawar da ya bayar wajen
tabbatuwar wannan taron a jiharsa, ya kuma
gode wa Sanata Rabiu Musa Kwankwazo a bisa
halartar taron da ya yi, sauran wadanda suka
samu godiya ta musamman kamar yadda Shehin ya ce sun taimaka wajen samun taron na bana
har da Sanata Shehu Sani da sauran wadanda ya
ce ba za su misaltu ba, sai dai ya nuna godiyarsa
ga dukkanin wadanda suka dafa wajen kammaluwar taron na bana
.
Source by @leadershipayau

COMMENTS

Name

Al'ajabi,13,Android zone,69,Applications,3,Aure,25,Blogger zone,1,computer zone,4,Dadin Kowa sabon salo,27,Facebook zone,12,Free Browsing,2,Hausa Films,1,Hausa novels,1,hotuna,2,Java zone,15,Kannywood,55,kiwon lafiya,35,Mata,12,Musics,24,Network,21,News,146,others,16,siyasa,81,Soyayya,3,Symbian zone,5,Video clips,33,video tutorials,3,Whatsapp,1,
ltr
item
Ameer: Bunkasar Shehu Inyass Ce Ta Sabbaba Yin Maulidinsa A Abuja Da Kaduna - Sheikh Dahiru Bauchi
Bunkasar Shehu Inyass Ce Ta Sabbaba Yin Maulidinsa A Abuja Da Kaduna - Sheikh Dahiru Bauchi
http://fm.nextwapblog.com/files/6475/dahiru-bauchi.jpg
Ameer
https://ameeryau.blogspot.com/2018/04/bunkasar-shehu-inyass-ce-ta-sabbaba-yin.html
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/2018/04/bunkasar-shehu-inyass-ce-ta-sabbaba-yin.html
true
2994989324915487916
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy