Rundunar tsaron Nijeriya ta NSCDC, a jihar Yobe ta damke wani mutum dan kimanin shekara 45- Shu’ibu Yakubu, wanda take zargi da yiwa yar she...
Rundunar tsaron Nijeriya ta NSCDC, a jihar Yobe ta
damke wani mutum dan kimanin shekara 45-
Shu’ibu Yakubu, wanda take zargi da yiwa yar
shekaru hudu (4) a duniya fyade, a Damaturu
babban birnin jihar. Mista Ayinla Taiye Olowo, shi ne kwamandan
rundunar NSCDC kuma ya bayyana cewa,
mahaifiyar wannan yarinyar ce ta kawo musu
korafi dangane da al’amarin, ranar 27 ga watan
Maris, 2018, inda daga bisani suka cukumo
wanda ake zargin domin gudanar da bincike. Kwamandan ya ci gaba da bayyana cewa,
binciken su ya gano cewar wanda ake zargin, ya
aikata wannan tabargaza ga karamar yarinyar ne
a sa’ilin da take wasar kasa a makwabta, yayin da
ya bata ‘alawar minti’, inda kuma daga bisani ya
dauke ta zuwa dakin sa tare da lalata da ita. “kamar yadda mahaifiyar ke gaya muna yadda
lamarin ya afku, ta ce bata ankara da wannan
al’amarin ba har sai a lokacin da take yiwa
yarinyar wanka, yayin da yarinyar ta nuna mata
cewa gaban ta yana yi mata radadi. Al’amarin da
ya sa mahaifiyar kokarin gano abinda ya faru, a karshe yarinyar ta shaida wa mahaifiyar kan
cewa wani mutum ne ya gaya mata, idan ta sake
ta fadi wanda yayi mata fyaden, to za ta mutu ne”. “Bugu da kari kuma, mahaifiyar tayi hanzari
wajen kai korafin ta ga jami’an mu, wanda kuma
kan ka ce kwabo sun kama shi. Kuma ba tare da
bata lokaci ba ya amsa laifin sa, tare da bayyana
cewa shima ba a hayyacin sa yake ba a sa’ilin da
ya yiwa yarinyar fyaden”. Ya nanata. Mista Taiye Olowo ya ce, baya ga yadda ya amsa
laifin sa ne, sai NSCDC ta tattara mai laifin da
karamar yarinyar zuwa asibiti domin a gudanar
da binciken lafiyar yarinyar tare da girman laifin. “bayan gudanar da gwaje-gwajen likita, an samu
dukkan su ba su dauke da Wata cuta wadda take
yaduwa ta hanyar jima’i (STD), sai dai kuma ya
yiwa ita yarinyar lahani kuma tuni aka yi mata
magani, wanda kuma daga bisani aka sallamo ta
zuwa gida”. Yayi karin haske. A hannu guda kuma, kwamandan ya bayyana
matukar damuwar sa dangane da yadda matsalar
yawaitar fyaden ke neman zama ruwan dare a
garuruwan Potiskum da Damaturu dake jihar ta
Yobe, inda kuma ya shawarci iyaye da cewa su
rinka yin kaffa-kaffa da yayan su, domin kaucewa fadawa a hannun bata-gari masu
kokarin bata rayuwar kananan yara. “miyagun mutane suna nan a kowanne lungu da
kwararo, kuma su kan yi amfani da kowacce irin
dama suka samu wajen aiwatar da alkaba’in nasu
da nufin cimma muradin su- na tsafi ko zina.” Ta
bakin shi
.
Source by leadershipayau
COMMENTS