Blog Archive

Powered by Blogger.

Adam A Zango Ya Koka Kan Nada Koredo Bello Sarkin Mawakan Arewa

Shahararren jarumi, mawaki makadi a farfajiyar shirya finafinan Hausa, watau Kannywood, Adam Abdullahi Zango, ya bayyana takaicinsa kan yadd...



Shahararren jarumi, mawaki makadi a farfajiyar
shirya finafinan Hausa, watau Kannywood, Adam
Abdullahi Zango, ya bayyana takaicinsa kan
yadda aka wasu rahotanni suke zagayawa cewar
an nada mawakin Kudu, Korede Bello sarautar
Sarkin Mawakan Arewa a jihar Kano. Da farko dai mawaki Koredo ne ya fara sanya hoto a shafinsa na Instagram sanye da rawani da
kaya irin na sarauta, ya kuma rubuta Sarkin Waka
a kasan hoton. Hoton da ake zargin a a Kano aka
dauka yayin hawan Sallah. Adam Zango ya wallafa a shafinsa na Instagram
cewar an dade ana wulakanta mawakan Arewa,
saboda haka lokaci ya yi ya kamata su gane, su
farka daga baccin da suke yi. “Na dade da gane cewa mawakan arewa gyandir
ne, suna kona kansu su haska wasu. Lokacin ya
yi da ya kamata mu hankala don kar mu
wulakanta.” In ji Zango. Shi ma babban darakta Falalu Dorayi, ya yi dogon
sharhi a kan balahirar a shafinsa na Instagram,
inda ya kakkausan suka ga mahukunta Arewa
kan wannan lamari, har ma ya nuna rashin
dacewar hakan, domin akwai mawaka da masu
yawan gaske a Arewa da suke hidima ga manya, amma kuma ana kaurace masu a lokacin jin dadi. Falau Dorayi ya ce, ba halayyarsa ba ce shiga
sabgar da ba tasa ba, amma wannan karon dole
ne ya tsalma baki, domin kowa ya gida, gida ya
bar shi. Ga rubutunsa kamar haka. “Zan yi tsokaci akan hotunan da Koredo Bello ya
saka a Instagram yayin hawan sallah a Kano har
yana fadin ya zama Sarkin Waka. Duk da dai ba
hali na bane shiga sabgar mutane, wannan karo
zan fadi albarkacin bakina. “Ina magana ne akan nadin Sarautar SARKIN
WAKA da ake cewa an yi wa wani mawakin kudu
Koredo Bello a Kano. Idan ta tabbata kamar
yadda mawakin ya wallafa a shafinsa, to lallai
mawakan Hausa na Arewa sai addu’a. Na san
duk rashin basirar mawakanmu ba su yi lalacewar da sai an tsallaka Legas za a samo musu
Sarki ba. “Koda yake ba abin mamaki bane, da ma haka
manyan Arewan namu suke, lokacin bukatarsu
suke nemanmu, lokacin moriyar sai dai mu gani a
wajen ‘yan kudu. “Ina mamakin yadda ciki yake manta kyautar
jiya. Duk wahalar da mawaka ke yi akan masu
kudi, masu Sarauta, da ‘yan siyasa na Arewa
wajen yi musu wakokin yabo da kwarzanta su
abin takaici sai ka ga babu wani lada. “Tun da aka nada Sarkin Kano na yandu ‘Dan
Maje’, Nazir Sarkin Waka ya sashi a gaba da yabo
da kirari; a cikin waken ma akwai inda ya hararo
masa zama Sarkin Kano, kuma Allah da ikonsa ta
tabbata. “Bayan ya zama Sarkin Kano bai bar wake shi ba
har gobe. Kuma in za a yi adalci a duk wakokin
da aka yi wa Sarkin Kano ba na jin akwai wadda
ta kai ta Nazir Ahmad tasiri. “Tabbas Nazir ya fi Korede Bello cancantar
sarautar, duk da ba mu san irin kalaman da
Korede ya zuba a wakar da ya yi wa Sarkin ba.
Sarautar waka a garin Hausawa sai mai jin Hausa,
a tsallake a dauko wani ko Hausa cikakkiya ba ya
ji, bai taba yin waka da Hausa ba, bai yi wa Kano da Kanawa ko baiti daya ba, bai yi wa Sarkin
Kano waka ba, a ba shi wannan mukami? Shi ke
nan an ci yaki an bar mu da kuturun bawa. “A bayyane yake mafi yawan manyanmu na
Arewa suna mutunta ra’ayin ‘ya’yansu ne kawai,
su kuma ‘ya’yan nasu ba su girma a kasar ba ma,
ba su damu da komai na Hausa da Al’ada ba,
wannan ya sa Biki, Suna, Murnar Zagoyowar
Haihuwa, Murnar Kammala Karatu, Baiko da duk wani abin murna, sai ka ga an dauko mawakan
kudu suna baje kolinsu. Idan aka ce su dauko
mawakan Arewa sai su ce ‘yan kauye ne. “Idan har Nazir bai zama Sarkin Mawakan Sarkin
Kano ba, to ban ga wanda ya kai shi ba. Ku
girmama al’ummarku sai wata al’ummar ta
girmama ta. Ni na san don kudinku da kudin
‘ya’yanku suke zuwa sabgarku. A tallafi gida
kafin waje.” A ra’ayin Falulu Dorayi ke nan. Sai dai binciken da wakilinmu ya gudanar game
da wannan lamari, ya gano cewar har yanzu
babu wata tartibiyar magana game da wannan
nadi da ake cewa an yi wa Koredo Bello, domin
wata majiya daga Fadar Masarautar Kano ta ce,
mawakin hawan Sallah kawai ya yi a Kano, ba wai ya zo ne domin a nada shi sarauta ba.
.
Source @leadershipayau

COMMENTS

Name

Al'ajabi,13,Android zone,69,Applications,3,Aure,25,Blogger zone,1,computer zone,4,Dadin Kowa sabon salo,27,Facebook zone,12,Free Browsing,2,Hausa Films,1,Hausa novels,1,hotuna,2,Java zone,15,Kannywood,55,kiwon lafiya,35,Mata,12,Musics,24,Network,21,News,146,others,16,siyasa,81,Soyayya,3,Symbian zone,5,Video clips,33,video tutorials,3,Whatsapp,1,
ltr
item
Ameer: Adam A Zango Ya Koka Kan Nada Koredo Bello Sarkin Mawakan Arewa
Adam A Zango Ya Koka Kan Nada Koredo Bello Sarkin Mawakan Arewa
http://fm.nextwapblog.com/files/6475/zango.jpg
Ameer
https://ameeryau.blogspot.com/2018/04/adam-zango-ya-koka-kan-nada-koredo.html
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/2018/04/adam-zango-ya-koka-kan-nada-koredo.html
true
2994989324915487916
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy