Hukumomin Saudiyya sun yi barazanar hana 'yan Najeriya zuwa aikin hajjin bana, bisa fargabar cewa alhazan za su iya yada cutar zazabin L...
Hukumomin Saudiyya sun yi barazanar hana 'yan Najeriya zuwa aikin hajjin bana, bisa fargabar cewa alhazan za su iya yada cutar
zazabin Lassa, a cewar hukumar kula da aikin haji ta Najeriya.
Akalla mutum 90 ne suka hallaka fiye da dubu daya kuma suka kamu da cutar a sassan kasar daban-daban a farkon shekarar nan. Alamomin cutar sun hada da zazabi, da amai, da gudawa, da ciwon kai, da na mara, da kuma ciwon wuya, da kumburin fuska. Kwayar cutar na bazuwa ne daga jikin wadanda suke cin berayen da ke dauke da kwayar cutar ko kuma abinci da ya hadu da kashi ko fitsarin bera. Hakazalika ana yi iya kamuwa da cutar idan jinin wanda yake dauke da kwayar cutar ya hadu da wanda bashi da shi ita. Mai magana da yawun hukumar, Musa Ubandawaki ya shaida wa BBC cewa, an gudanar da taro ranar Laraba da jami'ai daga jihohi 36 da jami'an hukumar na tarayya domin su tattauna kan yadda za a shawo kan barazanar da Saudiyya ta yi wa kasar. A jawabin da ministan lafiya kasar Farfesa Isaac Adewole ya yi a wajen taron, ya bayar da tabbacin ana bin matakan da duk suka kamata, don ganin an yi ingantaccen shirin da za a tabbatar don magance matsalar zazzabin Lassa a tsakanin maniyyata kasar.
.
Source: by @bbchausa.com
COMMENTS