Blog Archive

Powered by Blogger.

Duk Mabiyina Ya Fito Ya Yanki Katin Zabe Domin Kwatar ‘Yancinsa inji Shaikh Dahiru Bauchi

Babban Malamin darikar Tijjaniyyar a Nijeriya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya yi karin haske kan kiran da yake yi wa mabiyansa na su fito kan...



Babban Malamin darikar Tijjaniyyar a Nijeriya,
Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya yi karin haske
kan kiran da yake yi wa mabiyansa na su fito
kansu da kwarkwatansu wajen yankan katin
zabe na dindindin domin takadarwa don yin
amfani da wannan katin a zaben da ke tafe don aza nagartaccen mutumin da suka ga ya dace
kuma zai yi musu aiyukan da suka kamata. Shehu Dahiru Bauchi, wanda ya yi wannan karin
hasken a hirarsa da manema labaru a gidansa da
ke Bauchi a ranar Talatar nan, yana mai cewa,
Nijeriya kasa ce wacce kowa na da ikon yin
zaben da ya dace da shi domin kafa wanda zai
biya masa dukkanin bukatunsa ta hanyar shugabanci. Ya bayyana cewar ta wannan hanyar ne kadai
dan Nijeriya zai iya yakar wanda bai so kuma
cikin sauki domin a cewarsa zabar shugaba na
gari tamkar bayar da dama ce wajen wanzar da
shugabanci na gari, don haka ne ya umurci
mabiyansa da cewa; “Dukkanin mutanenmu su fito su yanki katin zabe,” a ta bakinsa. Shehi ya bayyana cewar kasar Nijeriya kasar su
ce don haka suna da hakkin fitowa domin neman
wanda suke so, hade da dabar mutumin da suka
tabbatar zai yi musu aiyukan da suka zabe sa don
su. Ta bakinsa yake cewa Nijeriya musulmi da kirista
kowa na da zarafin zabin da yake so ta fuskacin
shugabanci, “Ai kasar Nijeriya ta musulmi ne da
wanda ba musulmi ba; waye zai yadar da
hakkinsa? Wani dai ba zai yada hakkinsa ba. tun
da abun ya zama yakin da ‘yar karamar takarda ake yi bada makami ba; ai ya yi sauki, ka je ka jefa
kuri’ar ka zabi wanda zai mallakeka wanda kuma
kake ganin alamar zai biya maka bukatarka a
zamanka na dan kasa,” In ji Dahiru Bauchi. Bauchi ya daura kuma da cewa kuri’ar mutum
makaminsa ce, domin da kuri’a mutum ka iya
kashe kansa ko ya yanka kansa, don haka ne ya
bukaci kowa ya yi amfani da wannan makamin
tasa wajen zabar na gari, “Wai wasu ‘yan siyasa
suna cewa kuri’arka-‘yancinka. Ni kuma ba haka nake cewa ba. ni ba dan siyasa bane, amma abun
da na ke cewa, shi ne kuri’arka makaminka,
wukarka ka bai wa wanda zai yanka ka ko kuma
wanda zai yanka maka. “Masoyinka wanda yake sonka zai yanka maka
in ka bashi kuri’arka zai yanka maka, makiyinka
ko kuma masoyinka na suna idan ka ba shi
wannan kuri’ar to soyaka zai yi kuma ya yanka
ka. Soboda haka ka san fuskokin mutune tun
daga farko, ka san masoyinka ka san makiyinka. Dukkaninmu ‘yan Nijeriya mun san masoyanmu
da kuma makiyanmu, mun san su, sai in lokacin
kada kuri’ar idan ya kammala yi sai mu kada ma
wanda muke so,” in ji Shi. Daga bisani ya kuma nemi dukkanin wani dan
Nijeriya da ya fito fagen zabe domin zabar na gari
a kowani lokaci. Da ya juya kan shuwagabanin kuwa, Shehu
Dahiru Bauchi ya gargadi shugabanni kan
wadanda suke shugabanta domin a cewarsa
kowani shugaba ya dace ne ya tabbatar da cika
alkawuran da ya yi wa jama’arsa a lokacin yakin
neman zabe “Ainuhin abun da ake nufi da gwamnati musamman gwamnatin siyasa, jama’a
ne idan suna da wasu abubuwan da ba za su iya
samu ba sai su nemi gwamnati ta hanyar siyasa,
su kuma ‘yan siyasa za su nemi yin aiyukan da za
su kare mutane daga sharri da kuma samar musu
da alherin da suke bukata. in an zabi gwamnati ba ta kawo alheri ba sai sharri, ba ta ture sharri ba
sai alheri ta ture wannan ai ba gwamnati bace, a
don haka ne muke jawo hankulan mutane su yi
karatun ta nutsu,”. Ya bayyana cewar duk wanda ya fito gaban
jama’a aka kada masa kuri’a ya ci ya kamata ya yi
dukkanin mai iyuwa domin rage wa jama’ansa
matsatsin da suke ciki “Ana wahala don haka
muna kira ga gwamnati ta yi duk mai iyuwa
domin rage wa jama’a halalhalun da suke ciki domin a samu gudunar da shuganci yadda ya
dace,” kamar yadda ya ce.
.
Source by @hausaleadershi

COMMENTS

Name

Al'ajabi,13,Android zone,69,Applications,3,Aure,25,Blogger zone,1,computer zone,4,Dadin Kowa sabon salo,27,Facebook zone,12,Free Browsing,2,Hausa Films,1,Hausa novels,1,hotuna,2,Java zone,15,Kannywood,55,kiwon lafiya,35,Mata,12,Musics,24,Network,21,News,146,others,16,siyasa,81,Soyayya,3,Symbian zone,5,Video clips,33,video tutorials,3,Whatsapp,1,
ltr
item
Ameer: Duk Mabiyina Ya Fito Ya Yanki Katin Zabe Domin Kwatar ‘Yancinsa inji Shaikh Dahiru Bauchi
Duk Mabiyina Ya Fito Ya Yanki Katin Zabe Domin Kwatar ‘Yancinsa inji Shaikh Dahiru Bauchi
http://fm.nextwapblog.com/files/6475/dahiru-bauchi.jpg
Ameer
https://ameeryau.blogspot.com/2018/04/duk-mabiyina-ya-fito-ya-yanki-katin.html
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/2018/04/duk-mabiyina-ya-fito-ya-yanki-katin.html
true
2994989324915487916
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy