Blog Archive

Powered by Blogger.

Ni ban caccaki Atiku Abubakar ba Inji Rahama Sadau

Fitacciyar jarumar fina-finan Hausa da kuma na Turanci, Rahama Sadau ta karyata jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa ta caccaki...



Fitacciyar jarumar fina-finan Hausa da kuma na Turanci, Rahama Sadau ta karyata jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa ta caccaki tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar kan martanin da ya mayar wa Shugaba Muhammad Buhari na cewa matasan Najeriya ’yan cima zaune ne. A cikin wata sanarwa da jaruma ta aiko wa Aminiya a yau Laraba, ta bayyana cewa ita ba ta zabi wani dan takara a zaben shugaban kasa na 2019 mai zuwa ba, duk da cewa tana da ’yancin yin hakan a matsayinta na ’yar kasa. Jarumar wadda ta taka muhimmiyar rawa a cikin fim din ‘Sons of the Caliphate’ mai dogon zango da ake nunawa a gidan talabijin na Ebony, ta bayyana cewa cikin takaici ne ta rubuta sakonta don ta karyata batun jita-jitar da ake yadawa cewa ta caccaki jam’iyyar PDP ko kuma wadansu daga cikin ’yan takararta da ke neman shugabancin kasar nan. Jarumar ta ce, tana alfahari da kasancewarta ’yar Najeriya, kuma tana da ’yancin fadar albarkacin bakinta da kuma na zabe kamar kowa, amma ba tsarinta ba ne ta bayyana ra’ayinta a siyasa ta hanyar kalaman cin fuska ko batanci. Rahama Sadau wadda ta fito a manyan fina-finan Hausa da suka haxa da 'Rariya' da 'Shakka' da kuma 'Kanwar Dubarudu' ta bayyana bakin cikinta kan yadda waxansu mutane ke yaxa jita-jita ba tare da tabbatar da sahihanci labarin daga wurinta ba. Ta ce, “Ba ni da wata jam’iyya, ban kuma zabi wani dan takara ba, ba na kuma wata kungiya da ta jibanci siysasa ko cikin wata tafiya ta siyasa, ina so in sanar da mutane cewa ban yi hira da wata kafar yada labarai dangane da labarin da ake yadawa ba.
Babu wani abu na labarin da ake yadawa da yake gaskiya.” Jarumar ta bukaci al’umma cewa kada su yarda da labarin da suka gani ana yadawa, sannan ta gargadi wadanda suka kirkiro labaran da su daina bata mata suna. “Ina kira ga kafafen yada labarai da su tsaya a kan aikinsu kamar yadda ka’idojin aikin jarida ya shimfida, sannan duk wani abu da suka gani an alakanta shi da ni, to su rika tuntuba ta don su tabbatar da sahihancinsa ko akasin hakan. Na gode, Allah Ya yi muku albarka.” Inji jarumar.
.
Copyright @aminiya

COMMENTS

Name

Al'ajabi,13,Android zone,69,Applications,3,Aure,25,Blogger zone,1,computer zone,4,Dadin Kowa sabon salo,27,Facebook zone,12,Free Browsing,2,Hausa Films,1,Hausa novels,1,hotuna,2,Java zone,15,Kannywood,55,kiwon lafiya,35,Mata,12,Musics,24,Network,21,News,146,others,16,siyasa,81,Soyayya,3,Symbian zone,5,Video clips,33,video tutorials,3,Whatsapp,1,
ltr
item
Ameer: Ni ban caccaki Atiku Abubakar ba Inji Rahama Sadau
Ni ban caccaki Atiku Abubakar ba Inji Rahama Sadau
http://fm.nextwapblog.com/files/6475/rahama-sadau.jpg
Ameer
https://ameeryau.blogspot.com/2018/04/ni-ban-caccaki-atiku-abubakar-ba-inji.html
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/2018/04/ni-ban-caccaki-atiku-abubakar-ba-inji.html
true
2994989324915487916
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy