Tun daga farkon makon nan, dubban daruruwan al’ummar Musulmi musamman ‘Yan Darikar Tijjaniyya suka fara tururuwa a Kaduna domin halartar bik...
Tun daga farkon makon nan, dubban daruruwan
al’ummar Musulmi musamman ‘Yan Darikar
Tijjaniyya suka fara tururuwa a Kaduna domin
halartar bikin Mauludin Shehu Ibrahim Inyass na
kasa da aka saba yi a duk shekara. Mauludin na bana shi ne karo na biyu da Jihar
Kaduna ke karbar bakuncinsa tun daga lokacin
da aka fara yi a shekarar 1986. Bisa al’adar taron, a kan fara hidindimunsa tare
da gabatar da laccoci a kan abin da ya shafi
rayuwar Shehin malamin na tsawon kwana shida
ko biyar inda ake gayyato masana su yi bayani a
game da rayuwar Shehin na Tijjaniyya. Da kadan-kadan mutane ke fara halarta, yayin da
ya rage saura kwana daya taron kuwa, rukuni-
rukuni, tawaga-tawaga mutane ke tururuwa
zuwa garin da ke karbar bakuncin taron wanda a
bana an kiyasta akallamutum milyan uku za su
halarci taron. LEADERSHIP A Yau Juma’a ta tuntubi shugaban
karamin kwamitin shirya Mauludin na Kaduna,
Alhaji Lawal Salihu Malami domin karin haske
game da taron. “Hakika wannan taron na Mauludin Shehu
Ibrahim na kasa shi ne babban taron Musulunci
da babu kamar sa, ba kawai a Nijeriya ba har da
Afirka bakidaya. Babban makasudin yin Mauludin
shi ne murna da samun Shehu Ibrahim Inyass
wanda ba a yi Waliyyi Bawan Allah kamar sa ba a karne na 20. Kamar yadda aka saba, milyoyyin
al’umma ne za su halarci taron. A kowace
shekara Kungiyar Majma’u Ahbabu Shehu
Ibrahim ne suke shirya taron wadda kungiya ce
ta Musulunci, zalla masoya Shehu Ibrahim Inyass.
A bana muna godiya ga Allah a Kaduna za a yi taron wanda shi ne karo na 32 kuma wanda ya
nuna cika shekara 117 da haihuwar Shehu. Tuni
aka fara gudanar da tarurruka na Mauludin a
ranar 9 ga watan 4, shekarar 2018 tare da
gabatar da shiri kai tsaye a gidan talbijin da
radiyo na Liberty. Manyan Malamai da Shehunai suke gabatar da laccoci domin karantar da
mutane kyawawan halayen Shehu Ibrahim
Inyass. Haka nan don Shehunan su karantar da
al’umma zaman lafiya a tsakanin addinai da kuma
kwanciyar hankali a tsakanin al’umma domin
samun cigaba irin yadda Shehun ya yi a rayuwarsa”. Da aka tambaye shi, cewa wasu mutane suna
ganin taron muhimmancinsa kalilan ne saboda
mutane ba su amfana a zahiri da shi, maimakon
haka ma sai a hana su sakat kan neman
abincinsu saboda cunkoson jama’a da ake samu
a duk inda za a yi taron, ko ba ya ganin masu fadar haka suna da gaskiya? Alhaji Lawal ya amsa da cewa, “A’a, ba gaskiya ba
ne. Ai bisa yadda tun da aka fara taron daga
1986 ba a taba fasawa ba, ya nuna baro-baro a
fili irin alfanun da taron yake da shi. Taron yana
koyar da mutane Musulmi da wanda ba Musulmi
ba su yi koyi da irin jinkan da Shehu Ibrahim ya shimfida a duniya. Haka nan da yake Shehu
Ibrahim jagora ne wurin jaddada Sunnar Annabi
SAW, Musulmi za su amfana sosai daga
abubuwan koyi da ya aiwatar a rayuwarsa. Bugu
da kari a duk inda za a yi taron sai ka ga tattalin
arzikin wurin ya habaka saboda ‘yan kasuwa da masu sayayya da za su shigo. Sannan a wurin
taron ana yi wa Nijeriya addu’o’i na musamman
domin bunkasar cigabanta da kuma zaman
lafiya”. Shugaban kwamitin ya kuma ce saboda yawan
jama’ar da za su halarta, sun yi tanadin tsaro a
lungu da sako na sassan da suke dajibi da taron. “Alhamdulillah, kamar yadda kowa ya sani ne, shi
wannan taron babu wanda zai iya cewa ga
adadin mutanen da za su halarta, Khalifofi,
Almajirai da Masoya Shehu Ibrahim duk za su
halarta. Don haka muka bukaci jami’an tsaro su
taimaka mana da tsaro a sassan wurin da za a yi taron na Murtala Skuare. Sannan ‘ya’yan Shehu da
za su zo daga Senigal an musu kyakkyawan
masaukai, bayan haka muna daukar dukkan
matakan da suka kamata domin ganin taron ya
samu nasara, insha Allahu”, in ji shi. Kasancewar wasu lokuta ana samun hadurran
motoci a kan hanyar zuwa taron, ko akwai wani
mataki na rigakafi da masu shirya taron suka
dauka domin akalla a samu saukin lamarin a
bana? Y ace, “To, ba zan ce ba a samun hadurra
ba amma ba sosai ba ne. Kuma domin kauce wa hakan, Malamai da Mukaddamai suna wa masu
zuwa taron hudubobi a kan cewa a bi sannu ban
da mugun gudu wurin tafiya da dawowa, kuma
insha Allah mutane za su yi aiki da abin da aka
fada musu. Alhaji Lawal Malami ya yi amfani da wannan
damar wurin gode wa wadanda suka tallafa
domin samun nasarar taron, inda ya kara da
cewa, “ Muna addu’ar Allah ya sa mu yi taron
lafiya mu tashi lafiya. Allah ya kawo mutane lafiya,
ya koma da su gidajensu lafiya. Sannan muna godiya ga duk wadanda suka taimaka ta kowace
fuska don samun nasarar taron na Mauludin
Shehu musamman Gwamnatin Jihar Kaduna bisa
jagorancin Malam Nasir el-Rufa’i da ta ba mu
goyon baya da taimako. Allah ya saka wa kowa
da alkhairi”, a ta bakinsa. A halin da ake ciki kuma, daya daga cikin
Shehunan da suka gabatar da karatu a Gidan
Talbijin da Radiyo na Liberty, Sayyid Isma’il Umar
Almaddah wanda ya yi bayani a game da tafiye-
tafiyen da Shehu Ibrahim ya yi a kasashen duniya
a Larabar nan, ya yi kira ga masu neman raba kawunan al’umma su yi wa kansu kiyamullaili su
bari, inda ya kara da cewa “Jama’ar Shehu ‘Yan
Faila daya ne, kuma duk wanda ya ce zai raba
kansu ba zai iya ba amma idan mutum ya ga zai
iya, ga fili ga mai doki nan”. A wani labarin har ila yau, a yayin da yake
shugabantar taron Laccar Mauludin a zauren taro
na Gidan Arewa da ke Unguwar Sarki Kaduna,
Alkalin Alkalai na Kotun Shari’ar Musulunci ta
Jihar Kaduna, Dakta Shehu Ibrahim Ahmad, ya
bayyana Shehu Ibrahim Inyass a matsayin babban malamin da ya fi yada Darikar Tijjaniyya a
ko ina a fadin duniya. “Waliyyin Allah, yana da almajirai a ko ina a fadi
duniya wanda zukatansu suka hadu wuri guda
cikin soyayya saboda Allah. Wannan Bawan Allah
ya kai matsayin da ma a nan Nijeriya ya samar da
wata al’umma wadda duk wani jami’in tsaro idan
ya hadu da su koyaushe kuma a ko ina zai girmama su sannan ya ce “wadannan mutane ba
masu tayar da fitina ba ne”. Wannan manuniya ce
kan yadda almajiransa suka iya zama da kowa a
cikin al’umma bisa aminci”, ya bayyana. Alkalin Alkalan ya ce duk da yawan kabilun da
ake da su a Nijeriya, almajiran Shehu Ibrahim ana
samunsu a cikin galibinsu (kabilun). “Ina tunanin akwai kabilu guda 400 ko fiye da
haka masu yaruka daban-daban amma za ka
samu a kusan cikin dukkansu akwai ‘Yan
Tijjaniyya. Wannan daya ne daga cikin
karamomin Sahibul Faidhati. Shi ya sa nake
tunanin ina ma babban taken taron Mauludin na bana ya kasance ‘Idan akwai mai irin wannan
Shehin ya kawo shi mu gani’”. Tun da farko a kasididar da ya gabatar mai taken
“Shari’a da Hakika”, Dakta Abdulkarim Dayyib na
Sashen Nazarin Lissafi daga Jami’ar Ahmadu Bello
ta Zariya, ya yi kira ga ko wane Dan Darika ya
nemi Shehin da zai rike hannunsa domin yin koyi
da rayuwar Shehu Ibrahim Inyass. Sauran wadanda suka yi karin bayani kan
kasidar, sun ce wajibi ne Shehunan al’umma su
rika gudanar da rayuwa a bar koyi domin
kasancewarsu masu tarbiyyantarwa. Hidindinmun Mauludin na cigaba da gudana inda
a gobe Asabar, milyoyin al’ummar da ta halarci
taron za ta yi dandazo a katafaren Filin Murtala
Sikwaya domin kammala taron na bana.
.
Source by leadershipayau
COMMENTS