Blog Archive

Powered by Blogger.

Matukar Buhari Bai Maimaita Mulkinsa Ba Nijeriya Za Ta Koma Gidan Jiya, Inji kungiyar BSCC

Wasu gungun matasa a jihar Bauchi (Bauchi State Concerned Citizens) sun fito kan titi a ranar Asabar inda suke kira ga shugaban Nijeriya Muh...



Wasu gungun matasa a jihar Bauchi (Bauchi State
Concerned Citizens) sun fito kan titi a ranar
Asabar inda suke kira ga shugaban Nijeriya
Muhammad Buhari da ya fito ya sake neman
kujerar shugaban kasa a karo na biyu, domin
maimata shugabancin kasar nan. Kungiyar ta bayyana cewar matukar shugaban
Nijeriyan bai fito a karo na biyu ba to la-shakka
Nijeriya za ta koma gidan jiya ne kawai “Idan bai
fito ba wadanda za su sake amsar mulkin kasar
nan za su lalata komai ne, don haka za mu sake
fadawa gidan jiya wanda mu kuma bamu fatan hakan,” In ji masu gangamin nuna gamsuwa da
mulkin Buhari. Gangamin gangankon matasa masu nuna wa
shugaba Buhari goyon baya da gamsuwarsu da
salon mulkinsa, sun fara macin din nasu ne daga
titin karamar hukumar Bauchi kusa da
masarautar Bauchi inda suka yi tattaki zuwa cikin
manya titinan jihar dauke da hotunan Buhari da kuma sakonin da suke nuna cewar ya maimaita
kawai. Da yake ganawa da manema labaru, Sakataren
kungiyar da ke mara wa Buhari baya, ‘Bauchi
State Concerned Citizens’ Comrade Alkasim
Abdulkadir ya bayyana cewar shugaban Nijeriya
a kashin kansa mutum ne mai son ganin an samu
ci gaba da fid da Nijeriya daga halin da take ciki, amma abun takaici wadanda suke zagaye da shi
ba damuwarsu ci gaba ba ne “mutum daya ba zai
iya gyara kasar nan ba, don haka dole ne idan
muka hango muka ce Baba a waiwayi waje kaza
Baba ka saurare mu kawai domin a jikanka
akwai wadanda basu da wani nufi illa kawo maka cikas mu kuma ba za mu lamunta ba,” “Baba idan muka ce maka kalli gabanka, ka kalla
kawai domin a samu gyara a Nijeriya,” In ji
Sakataren. Kwamared Alkasim Abdulkadir ya bayyana
cewar jihar Bauchi da shiyyar Arewa Maso Gabas
sun gamsu dari bisa dari da mulkin shugaban
Nijeriya Buhari a bisa hake ne ma za su yi ta yin
duk mai iyuwa har sai shugaban Nijeriya ya amsa
zai sake tsayawa takarar shugaban kasa a 2019. Alkasim Abdulkadir ya ce jihar Bauchi ta samu
kulawa sosai daga Buhari a sakamako jihar tana
daya daga cikin jihohin da ta ke son Buhari fiye
da misali, don haka ne Buhari ya yi kokarin bayar
da mukamai wa wasu ‘yan jihar da nufin
taimakon jihar “Mu matasa muna shaida wa Buhari cewar wadanda ya basu mukaman nan ba
su yi mana komai, domin daga cikin wadanda
Buhari ya basu mukamai sama da ashirin amma
kalilan ne daga cikinsu suke kawo wa jihar ci
gaba, don haka muna kira garesu da su fa sani
ido na kansu,” Dangane da martaninsu ga tsohon Ministan
Tsaro, Janaral TY Danjuma, Sakataren masu
gangamin nuna goyon bayan Buharin ya bukaci
shugaban Nijeriya da ya gaggauta kamewa gami
da hukunta TY kan munanan kalaman da ya yi
wadanda ka iya kawo wa Nijeriya munanan matsaloli musamman don tayar a rikici. Ya ce, “Kalaman da TY Danjuma ya yi wadannan
kalaman babu dattako sam a ciki, sannan kalamai
ne wadanda shugaban Nijeriya ya kamata ya
tashi tsaye ya yi hukunci, sannan hukuma su
kirasa su yi masa hukunci,” Ya ce, “idan har gwamnati za ta iya kama Kanu
don yana barazana wa tsaro meye sa ba za a iya
kama Danjuma ba domin kamalansa suna neman
kawo tashin hankali,” Ya bukaci TY Danjuma da ya gaggauta neman
yafiya a wajen ‘yan kasa a bisa kamalan da ya
furta na cewar ‘yan Nijeriya su kare kawukansu. Daga bisani ne kuma ya shaida cewar dandazon
matasan dukkaninsu magoya bayan Buhari ne
kuma za su ci gaba da mara masa baya har ya kai
ga samun nasara a zaben 2019. Daya daga cikin masu gangamin nuna goyon
bayan Buharin Abbas Tukur Ahmad ya bayyana
cewar salo da shugabanincin da Buhari ke yi abu
ne wanda kowani mutum ya kamata ya mara
masa domin Buhari ya dauko hanyar gyara kasar
nan ta kowace fuska
.
Source @leadershipAyau

COMMENTS

Name

Al'ajabi,13,Android zone,69,Applications,3,Aure,25,Blogger zone,1,computer zone,4,Dadin Kowa sabon salo,27,Facebook zone,12,Free Browsing,2,Hausa Films,1,Hausa novels,1,hotuna,2,Java zone,15,Kannywood,55,kiwon lafiya,35,Mata,12,Musics,24,Network,21,News,146,others,16,siyasa,81,Soyayya,3,Symbian zone,5,Video clips,33,video tutorials,3,Whatsapp,1,
ltr
item
Ameer: Matukar Buhari Bai Maimaita Mulkinsa Ba Nijeriya Za Ta Koma Gidan Jiya, Inji kungiyar BSCC
Matukar Buhari Bai Maimaita Mulkinsa Ba Nijeriya Za Ta Koma Gidan Jiya, Inji kungiyar BSCC
http://fm.nextwapblog.com/files/6475/buhari-001.jpg
Ameer
https://ameeryau.blogspot.com/2018/04/matukar-buhari-bai-maimaita-mulkinsa-ba.html
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/2018/04/matukar-buhari-bai-maimaita-mulkinsa-ba.html
true
2994989324915487916
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy