Idan ‘yan Nijeriyan nan uku dake zaune a kasar Amuka suka samu abin da suke so to lallai sunayensu zai kasance a katin jefa kuri’ar zaben sh...
Idan ‘yan Nijeriyan nan uku dake zaune a kasar
Amuka suka samu abin da suke so to lallai
sunayensu zai kasance a katin jefa kuri’ar zaben
shekarar 2019, haka kuma zai zama karo na
farko a tarihi da al’ummar Nijeriya dake zaune a
ketare suka nuna shawa’arsu suka kuma shiga harkar siyasar kasar nan gadan-gadan. A watan daya gabata ne Mista Gabriel Adegboye
da Mista Samuel Mbonu da kuma Mista Omoyele
Sowore suka kaddamar da yakin neman zaben
darewa kujerar shugabancin kasar nan a can
kasar da suke zaune ta Amurka. Amma duk sun
kaddamar da yakin neman zaben nasu ne daga can kasar Amurka a cikin ‘yan Nijeriya mazauna
can, hakan bai sa kungiyar ‘yan Nijeriya mazauna
kasashen waje ta “Nigerians in the Diaspora
(NIDO)” su rugume su ba, kungiya da
shugabannin ta su na nisanta kansu daga
wadanan ‘yan takaran. A watan Fabrairu Mista Mbonu, mazunin garin
Washington DC ya yi bukin sanar da bukatar sa
na shiga gwagwamayar takarar shugabancin
kasar nan a taron da aka yi a dakin taro na
“Airforce One Boardroom” dakin taro ne dake
cikin “Ronald Reagan Presidential Library” a garin California. Majiyar mu bai yi mana cikakken bayanin yadda
bikin nuna shaw’awar nasa ya gudana ba amma
wani shafin labarai na intanet mai suna Elombah
ya wallafa wasu mukala a watan Maris a kan
yakin neman zaben Mista Mbonu da kuma irin
tanadin da ya yi wa kasar nan in har ya samu cimma burinsa na zama shugaban Nijeriya. Haka kuma, kamar sun hada baki, Mista Sowore,
mawallafin shafin watsa labarai na Sahara
Reporters, da Mista Adegboye, wani Fasto sun
kaddamar da yakin neman zama shugaban
Nijeriya a rana daya wato ranar 10 ga watan
Maris a jihohin Amurka guda biyu da Maryland da Tedas. Mista Sowore ya kaddamar da taron yakin
neman zaben nasa ne a wani gidan cin abinci na
wani dan Nijeriya a birnin Bowie ta jihar Maryland
yayin da bayani ya nuna cewa Mista Adegboye ya
kaddamar da nasa taron yakin neman zaben ne a
gidansa dake Pflugerbille ta jihar Tedas. “Bamu san komai a kansu ba” inji Patience Key,
shubaban daraktocin kungiyoyin NIDO da USA.
“A hukumance kungiyar mu ta NIDO bata da
wani masaniya a kan wadannna ‘yan takara da
yakin neman zaben da suke yi” An kirkiro da kungiyar NIDO ce a shekarar 2000,
hadakar kwararrun ‘yan Nijeriya ce da
kungiyoyin kwadago da sauran kungiyoyi dake
zaune a kasashen waje da nufin samar da hanya
mafi sauki da ‘yan Nijeriya dake zaune a
kasashen wajen zasu yi mu’amala da gwamnatin da take mulki a Abuja. Tuni kungiyar ta rikida
daga yin ragistan kananan kungiyoyi zuwa yi wa
daidaikun mutane ta kuma fadada mazauninta
daga garin Atlanta da Georgia da Canada da
Europe zuwa Amurka ta Yamma da tsakiyar
Amurka. “A kan ‘yan Nijeriya dake zaune a kasashen
duniya, muna tattatara bayan kwarewarsu don
ganin yadda za a samu hadin kai ta taimakon
kasar mu Nijeriya. Kungiyar mu bata siyasa ba ce,
mu ba ‘yan siyasa bane, bamu kuma jingina da
wata kungiyar siyasa ba” inji Misis Key wadda kuma ita ce shugaban kungiyar NIDO na jihar
Maryland ta kasar Amurka. Sylbester Mode, shugaban kungiyar a jihar
Birginia, na da ra’ayin nesanta kungiyar daga
‘yan kasar dake da muradin siyasa mazauna
kasar Amurka dama sauran kasashen duniya. “Basa tare da kungiyar mu ta NIDO reshen
Amurka, saboda kawai suna zaune a nan kuma
suna takara bai mayar dasu cikinmu ba” inji shi. Mista Mode, wanda yana zaune a yankin
Washington DC ta kasar Amurka tun shekarar
1980, ya ce, a shekarun baya ‘yan Nijeriya masu
ra’ayin siyasa sun sha yin amfani da kugiyar
wajen cimma burinsu, ya tabbatar da cewar a
wannan lokacin ba zasu yarda a yi amfani dasu ba wajen cimma burin siyasa. “Da zaran sun isa Abuja, sai su shiga neman na
kansu, su manta da kungiyar mu ta NIDO.” Mista Mode ya kara da cewar, an yi wa kungiyar
NIDO ragista ce, a matsayin wata kungiyar da ba
zata tsunduma fagen harkokin siyasa ba kamar
dai yadda dokokin kasa Amurka ya tanada. “Mu ba ‘yan siyasa bane, sashi na 501 (c) 3 na
tsarin mulkinmu ya nuna cewa mu wata kungiya
ce mai zaman kanta ne wadda ba mai neman riba
ba, hakan na nufin ba zamu iya shiga fagen
siyasa ba” inji shi. Daga dukkan alamu, wadannna ‘yan takarar
basu zo a hukumance sun nemi goyon bayan mu
ba duk da cewa, wasu daga cikinsu su gaiyaci
daidaikun mutane a cikin kungiyar zuwa
tarukkan yakin neman zabensu, kungiyarmu ta
NIDO ta kuma gargadi manbobin ta a kan hada ra’ayoyinsu tare da ra’ayin kungiyarmu ta NIDO. “Babban kuskure ne in wani dan kungiya ya
halarci wani taron siyasa a matsayinsa na dan
kungiyar NIDO”, inji Misis Key, ta kuma kara da
cewar ta samu takardar gayyata zuwa taron
yakin neman zaben Mista Mbonu dana Mista
Sowore. “Na san Sowore, na yi magana da shi na kuma
gan shi lokacin da ya je yakin neman zabe a jihar
Maryland amma na je taron ne a matsayin kashin
kai na ba ina wakiltar wani bane” Shaharraren mai wallafa jaridar nan ta intanet mai
suna Sahara Reporters, Mista Omoyele Sowore a
kwai alamun cewar, fitowar Missta Sowore da
Mbonu da kuma Adeboye a matsayin masu
takarar kujerar shugabancin kasar nan ya kada
zukatan yan Nijeriya mazauna kasar Amurka fiye da yadda a ke tunani. A shekarun bayan, in
lokacin zabe ya yi sai dai ‘yan Nijeriya dake zaune
a kasar Amurka su karbi bakoncin ‘yan takaran
kujeran shuganci daga gida Nijeriya musamman
bayan an kamala zaben fid da gwani na jam’iyyu. A watan daya gabata ‘yan takaran nan guda uku
sun yi zagayen yakin neman zabe fiye da yadda
‘yan siyasa daga gida Nijeriya ke yi in shigo sai
abin takaicin sakon da suka yi kokari shigo da
bai kai ga inda ya kamata ba a tsakanin ‘yan
Nijeriya mazauna kasar Amurka. A sakon daya watsa dai-dai da fara yakin neman
zaben nasa, Mista Adegboye, ya ce, Shi malamin
addinin Krista ne kuma Allah ne ya kaddara
fitowarsa ya jagoranci Nijeriya domin fito da ita
daga rikice rikicen zubar da jini dana siyasa da
matsalar tattalin arziki, An haife shi ne a ranar 9 ga watan Agusta 1965, dan asalin garin
Ogbomoso, ta jihar Oyo, duk da cewar bai yi
cikakken bayanin yadda zai cimma wannan
manufa nashi ba amma ana saran in har ya kai ci
zai tabuka wani abu. Ya kuma ce , bai shiga wani
kungiyar siyasa ba a halin yanzu, sanan zai nufi gida Nijeriya ranar 10 ga watan Maris domin ci
gaba da yakin neman zabensa. A wani sakon daya tura ta kafar Youtube, Mista
Mbonu ya bayyana cewar, shi ba kamar sauran
‘yan siyasan Nijeriya bane zai kawo cikaken ci
gaba a kasar duk da cewa bai yi bayanin
hanyoyin da zai cimma wannan burin ba. Ya
shirya taro da ‘yan Nijeriya a garin Charlotte na jihar North Carolina ranar 9 ga watan Mayu domin
ya tattauna sakamakon ziyararsa zuwa gida
Nijeriya, ya mayar da hankali ne a kan abubuwa
guda uku a yakin neman zabensa wadanda suka
hada da samar da wutan lantarki da tsaftatacen
ruwan sha da kuma tsaro. Shi ko Mista Sowore, yakin neman zabensa yana
samun tagomashi ne saboda matsayinsa na
mawallafi, yana samun kabuwa a wajen ‘yan
Nijeriya mazauna Amurka, amma duk da haka
yawan mutanen dake bayansa bai kai abin azo a
gani ba in aka kwatanta da yawan ‘yan Nijeriya dake kasashen waje. Ya samu karbuwa kwarai da gaske a zagayen da
ya yin a jihohin Maryland da Pennsylbania da
kuma Michigan a watan Maris, amma irin yadda
aka karbi bukatar neman gudummawar daya
nema ba a bin a zo a gani bane shi ma. Ba a samu
cimma Dala Miliyan 2 da aka nema na tallafin yakin neman zabensa, amma tun da a kwai
sauran kwanaki kusan 300 kafin a gudanar da
zaben yana iya kaiwa ga ci
.
Source @leadershipayau

COMMENTS