Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana aniyarsa ta sake tsayawa takarar Gwamnan Jihar Kano a zaben shekara ta 2019, duk da cew...
Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje
ya bayyana aniyarsa ta sake tsayawa takarar
Gwamnan Jihar Kano a zaben shekara ta 2019,
duk da cewar Gwamnan har yanzu shelanta
hakan ba, amma dai ya bayyana hakan ne wata
tattaunawa da gidan Talbijin na Channel TB. Yace daga dukkan abubuwan da na ke gani a kasa
tare da yakinin yadda na ke da tabbatacin yadda
ci gaban Jihar Kano ya ke gudana a halin yanzu,
musamman bukatar da muke da ita na ganin
hakikanin yadda ci gaban jihar Kano ya kamata
ya kasance, ina ganin akwai bukatar ci gaba a zango na biyu . Na tabbata ayyukan da muka fara da kuma
wadanda muka kammala ina ganin dama ce
kwakkwara idan aka sake samun karin wasu
shekarun hudu su cika shekaru takwas. Gwamna
Ganduje ya ci gaba da cewa yana daga cikin
dalilan yanke shawarar sake tsayawa takarar Gwamnan Kano, sakamakon yawaitar kiranye
kiranye da magoya baya ke tayi na bukatar mu
sake tsayawa wannan takara. Hakazalika Gwamna Ganduje ya bayyana cewa
shekaru hudu ba zasu isa ba ga kowacce irin
gwamnati wajen sanya tabbataccen ci gaban
bisa doron kowacce irin siyasa a Kasar nan,
Gwamna Ganduje ya haskawa jama’a cewar ko
da kundin tsarin mulkin kasa ya aminta da sake neman karin wa’adin shekaru hudu. Gwamna Ganduje ya kuma yi tsokaci kan
matsaloli nan da can da suka daibaibaye
Jam’iyyar ta APC a wannan lokaci, ciki harda
batun kara wa’adin shuganbanci ga
shugabannin Jam’iyyar a matakin kasa, saboda
haka sai Gwamna Ganduje ya yabawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari sakamakon shiga
tsakanin da ya yi cikin al’amarin, inda ya bayyana
cewa babu wani laifi idan uwar Jam’iyyar ta
shirya gudanar da babban taron ta na kasa
domin kaucewa abin ka iya kawo cikas ga
nasarar Jamiyyar. Ya kara da cewa shi kansa kundin tsarin mulkkin
Jam’iyyar APC bai amince da karin wa’adin
shugabanci ba haka kuma ya ne santa kansa da
wannan, babu wata damar karin wa’adin
shugabanci ga Jam’iyyun a cikin kundin tsarin
mulkin Najriya. Gwamnan ya yi la’akari da cewar ba’a raba jam’iyya da rarrabuwar fahimta duk da
cewar akwai kyakkyawan fatan daidaita wanann
sabani .Da yake tsokaci kan wasu abubuwa da
suka shafi Gwamnonin Jam’iyyar APC, Ganduje
cewa ya yi a tunani na akwai yarjejeniya, duk da
cewar wannan matsalar ba wai don zaben shekara 2019 ta ke faruwa ba. Amma dai wasu
mutanen na da tunanin cewa idan muka tafi
taron kasa a haka, musamman ganin akwai tarin
matsaloli nan da can, ana zaton kila hakan ya kai
ga rabuwar Jam’iyyar, wannan kuma harsashe
ne kawai, ya iya zama hakan ko akasin haka.
.
Source: hausaleadership
COMMENTS