Barkanmu da wannan lokaci, to kamar de yadda wasunku sun riga da sunsan wannan hanyar ta kunna fitila na wayarka ta android ta hanyar tafa h...
Barkanmu da wannan lokaci, to kamar de yadda wasunku sun riga da sunsan wannan hanyar ta kunna fitila na wayarka ta android ta hanyar tafa hannu wato (clap) ba tare dakun ta6a wayar takuba, nasan wannan zai baku mamaki, to amma tunda kuna tare damu zaku Rinka samun abubuwan ban mamaki,
to idan kanaso ka seta wayarka tana abin dana fada wato idan kayi tafi flashlight ya kunna sannan idan kayi tafi ya kashe kansa, to abin da zakuyi shine,
.
Kuje play store ko google, kuyi download na wannan App mai Suna ==> SPEAK TO TORCH LIGHT <== ko ==> CLAP TO FLASH <== Shi wannan application da shine ake sanya waya tayi abin da muka fada, sabo da haka da zarar kunyi download dinsa, sai kuyi install dinsa saiku budeshi zakuga inda aka Rubuta ==>START<== to saiku ta6a wajen da zarar kun ta6a zai nunu muku wani shafi wanda zakuga hoton hannu yana ta tafi, to kaima saika gwada tafa hannunka, da zarar ka tafa zakaga flashLight dinka ta kawo, da zarar ka sake tafawa zakaga ta dauke, shikkenan haka zaku rinkayi idan zaku kunna flashlight ta hanyar tafa hannu
.
Allah ya bada sa,a
COMMENTS